Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe
Ƙungiyar mata Musulmai masu larurar ji a Najeriya ta ƙasa The Association of Deaf Muslim Women in Nigeria (ADMUN) ta gudanar da taron ta na ƙasa karo na 12 a Jihar Gombe, tare da kira mai ƙarfi ga hukumomi da ƙungiyoyi masu zaman kansu da su samar da tsare-tsare da zasu haɗa kowa da kowa, domin tallafawa mata Musulmi kurame a faɗin ƙasar nan.
An gudanar da taron na kwanaki uku ne mai taken: “Ƙarfafa Mata Musulmi Kurame ta Hanyar Imani, Ilimi da Haɗin Kai,” tare da haɗin gwiwar ƙungiyar haɗakar mata Musulmi ta Gombe.
Mahalarta daga jihohi daban-daban ne suka halarta, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi addini, rayuwa da ci gaba na mata masu larurar ji.
A jawabin ta na buɗe taron, Dokta Aisha Abubakar Kumo, shugabar ƙungiyar Muslim Sisters Organization (MSO) reshen Gombe, kuma malama a Sashen Nazarin Addini na Jami’ar Gombe, ta jaddada buƙatar samar da kayan koyon yaren kurame domin sauƙaƙa sadarwa da kuma samun ingantaccen ilimi ga waɗanda ke da larurar ji.
Ta kuma buƙaci majalisar dokoki ta kafa doka da za ta haramta wariya ga masu nakasa, tana mai nuna damuwa kan yadda har yanzu masu larurar ji ke fama da matsaloli wajen samun ilimin addini da na zamani.
Dokta Aisha ta bayyana rashin halartar wasu manyan baƙi da aka gayyata a matsayin abin takaici, musamman idan hakan na da nasaba da wariya ga masu larura.
A nasa jawabin, Dokta Dawud Muhammad ya yaba da irin jajircewar ADMUN wajen tallafawa mata Musulmi masu larurar ji.
Ya buƙaci a fara amfani da alamun magana wato sign language na kurame da kayan kallo a cikin masallatai, musamman a yayin huɗubar Juma’a, domin bada damar halartar ibada cikin fahimta.
Shugabar ƙungiyar ta ƙasa ta ADMUN, Malama Hajarat Nasir Maƙarfi, ta bayyana cewa manufar taron ita ce samar da ilimin addini da horo da ci gaban mata Musulmi kurame.
Ta bayyana cewa har yanzu akwai ƙalubale da dama da ke fuskantar waɗannan mata, ciki har da ƙarancin damar samun ilimi, rashin haɗuwa da al’umma da kuma yawaitar rashin aikin yi.
Malama Hajarat ta roƙi a samar da tallafin karatu, cibiyoyin koyon sana’o’i da shirye-shiryen tallafi da suka dace domin inganta rayuwar mata kurame.
Ta kuma buƙaci hukumomin gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kansu da su samar da kuɗaɗe da kayan aiki don tabbatar da ɗorewar ayyukan ADMUN a faɗin ƙasar.
Hajiya Aishatu Salisu Abdullahi, ɗaya daga cikin dattawan ƙungiyar, ta gode wa malamai, shugabannin al’umma bisa goyon baya da suke bai wa ƙungiyar.
Ta bayyana cewa tun kafuwarta a shekarar 1992, ADMUN ta shafe fiye da shekaru 30 tana fafutukar kare haƙƙin mata Musulmi masu larurar ji a Najeriya.
Mahalarta daga jihohin Gombe (inda aka gudanar da taron), Kaduna, Filato, Borno, Bauchi, Abuja, Nasarawa da Kwara sun halarci taron.
