Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Dikko Raɗɗa ya bada umurni ga dukkan zaɓaɓɓun wakilai da su saurari buƙatun al’ummar su wanda haka zai taimaka wa gwamnati a shirye shiryen da take na sauya fasalin kasafin kuɗin jihar na shekara ta 2026.
Mataimakin gwamnan jihar malam Faruk Lawal Jobe wanda ya wakilci gwamna Dikko Raɗɗa ya ƙaddamar da shirin a mazabar sa ta Ƙanƙara A da B dake a cikin ƙaramar hukumar Ƙanƙara.
A jawabinsa na buɗe taron mataimakin gwamnan, ya bayyana cewa” Gwamnan Jihar katsina shi ne, ya bada umarnin cewa” dukkan wanda aka zaɓa ko mai muƙamin gwamnati da ya koma mazaɓar shi domin halartar wannan taro.
“Akan haka ne muka zo mazaɓar mu domin ƙaddamar da wannan shiri a hukumance, kuma na ji ra’ayin al’umma da ke mazaɓu, a kan abinda suke buƙata, wanda za’a sanya masu a cikin kasafin kuɗin shekara ta 2026.
Malam Farouk Joɓe ya bayyana cewa wannan mataki zai sauya yadda ake tsarin kasafin kuɗi a Jihar Katsina.
Sai mataimakin gwamnan ya yi kira ga mahalarta taron da su tabbatar sun kawo buƙatun da suke ci ma al’umma tuwo a ƙwarya.
Shima a nashi jawabin kwamishinan kasafin kuɗi na jihar, Hon. Malik Anas ya bayyana cewa” Irin wannan shiri na jin ra’ayoyin jama’a shi ne na farko a Jihar Katsina, “saboda haka al’umma su tabbatar sun gabatar da abinda yake damun su domin a aiwatar masu dashi,”inji Anas
Kwamishinan ya cigaba da cewa” Ayyukan da gwamnatin ta ke yi sun kasu kashi uku, akwai wanda gwamnatin ƙaramar hukumar ta keyi, akwai na gwamnatin jihar da kuma na gwamnatin tarayya.
Saboda haka al’umma su sani, idan duk an tattara aiyyukan za’a duba, a bai wa kowanne ɓangare haƙƙin shi, domin ba shi damar gudanar da aikin da ya rataya akan shi ga al’umma.
Da yake ƙarin haske shugaban shirin cigaban al’umma na Jihar Katsina, Dr kamaladeen ya bayyana cewa” Gwamnatin Jihar Katsina ta kafa hukumar cigaban al’umma, wadda za ta taɓa al’ummar da ke karkara.
“Wannan yasa gwamnatin jihar Katsina, ta bada dama ga dukkan mazaɓu 361 da ke faɗin jihar, dasu gudanar da jin ra’ayin al’umma, akan buƙatunsu da su ke ci masu tuwo a ƙwarya,”inji kamaladdeen.
Al’umma da ƙungiyoyi da dama suka tofa albarkacin bakin su, akan buƙatun su wanda suka haɗa da ƙara samar da tsaro, inganta harkar ilimi da lafiya, cigaban al’umma da samar da ababen more rayuwa da sauran su.
Taron wanda ya guda a ofishin hukumar samar da ilimi na ƙaramar hukumar Ƙanƙara ya samu halartar shugaban ƙaramar hukuma Hon. Kasimu Dan Tsoho, mai bai wa gwamnan Jihar Katsina shawara kan ilimi mai zurfi Hon. Isa Muhammad, wakilan uwayen ƙasa.
