
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen Sama ta Ƙasa (NCAA) ta shigar ƙorafi ga Antoni Janar na Ƙasa (AGF), Lateef Fagbemi da Sufeton ƴan sanda Kayode Egbetokun, inda ta nemi su binciki mawaƙin Fuji, wato Wasiu Ayinde da aka fi sani da K1 De Ultimate bisa tsaurin ido da ya nuna a filin jiragen sama a Abuja, ranar Talata.
Kakakin NCAA, Michael Achimugu ya ce yunƙurin Ayinde na tare jirgin ValueJet da ke halin tafiya ya saɓa wa dokar gudanar da harkokin sufurin jiragen sama a Nijeriya.
A wata takarda zuwa ga AGF da Sufeton, NCAA ta yi kira da a gurfanar da kuma yin binciken aikata manyan laifuka akan K1 kamar yadda dokokin hukumar suka bada dama.
Da fari a yau Alhamis ne NCAA ta dakatar da mawaƙin daga harkokin jiragen sama na tsawon wata shida, inda ta yi gargaɗin duk kamfanin jirgin da ya ba shi damar tuƙi, akwai yiwuwar a ƙwace lasisinsa.
A ranar Laraba NCAA ta dakatar da matuƙa jiragen sama na ValueJet biyu kan tuƙin da ba a cika ƙa’ida akai ba, inda aka ga Ayinde a wani faifan bidiyo yana ƙoƙarin dakatar da jirgin.
