
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wata tawagar haɗakar masu ruwa da tsaki a Jihar Ribas ta bayyana rashin gamsuwa da shirin gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomin jihar, wanda ta a cewarta ya saɓa wa doka kuma barazana ne ga dimukraɗiyyar Nijeriya.
A wata buɗaɗɗiyar wasiƙa ga Shugaba Bola Tinubu, ƙungiyar, ƙarƙashin manyan jagororinta ta yi kira da a gaggauta dakatar da zaɓen, wanda aka shirya gudanarwa a ranar 30 ga watan Agusta, 2025.
Ƙungiyar ta zargi jagorancin siyasar jihar da yunƙurin saɓa wa hukunce-hukuncen doka da yin watsi da su don ganin an gudanar da zaɓen.
Daga cikin ƴan tawagar akwai Atedo Peterside, Celestine Omehia, Prince Uche Secondus, Cif Abiye Sekibo, Sanata Lee Maeba, Dakta Dakuku Peterside, Sanata Andrew Uchendu da kuma Injiniya Tele Ikuru.
Sun koka da yadda ake ƙoƙarin taka dokokin mulki, inda a cewarsu yunƙurin yin zaɓe a tsarin da shugabancin jihar ke tafiya a kai a yanzu ba daidai ba ne, saɓa wa tsarin dimukraɗiyya ne.
Haka kuma, sun bayyana cewa shirya zaɓen daga Kantoman Ribas, jefa dokokin jihar da na ƙasa ne cikin haɗari.
