Kano: Tsofaffin kansilolin APC sun yi zanga-zangar barranta kansu da kalaman shugaban APC, Abdullahi Abbas

Spread the love

Shugaban kungiyar tsoffin kansilolin Jam’iyyar APC wanda wasun su suka sauya sheƙa daga APC zuwa NNPP, sun musanta maganar da shugaban Jam’iyyar APC na Kano Abdullahi Abbas ya yi na cewa sun turo su ga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf domin yi musu yaƙin sunƙuru a siyasa da cewa ba gaskiya ba ne shiftin gizo ne kawai.

Sunusi Kata Madobi wanda shine shugaban kungiyar ne ya bayyana hakan yayin wani taron tattaki na musamman da tsofaffin kansilloli sama da 3000 suka gudanar cikin ma’aikatar yaɗa labarai da ayyukan cikin gida a sakatariyar Audu Bako.

Ya kuma ce, za su sakawa gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da halarci bisa halarcin da ya yi musu na maida su mutane.

Wasu daga cikin kansilolin da suka halarci taron sun bayyana mubaya’ar su ga gwamnan na Kano.

A nata ɓangaren, Hajiya Uwa Magaji Jiki Daga Bebeji ta ce kansilloli ne su ba yaran Abdullahi Abbas ba don haka magana da ya ke yi cewa sun turo su wanke gara ne, ba gaskiya ba ce, kyawawan halayen Gwamna Abba ne suka jawo hankalinsu suka zo cikin inuwarsa.

Shi ma Ɗahiru Yusuf daga Gezawa kuma tsohon kansila yace shima yana cikin wadanda tsohuwar gwamnatin Danduje ta hana hakkin su, don haka maganar Abdullahi Abbas ba gaskiya bane! Sun ga gwamna Abba zai jikan mu ne shine suke neman bata mana ruwa.

Da yake mayar da martani kan ziyarar da suka kai musu yace, mai girma Gwamna ya amince da cewar zai biya su hakkokin wanda gwamnatin baya ta kasa biyansu, kuma gwamnan yace baya bukatar sakamakon komai daga gare ku wai don ku koma jam’iyyar sa, a a yayi ne domin Allah.

Gwamnan ya ce magana ake ta Kano kawai kuma ku yan Kano ne, don haka maganar da Abdullahi Abbas yayi magana ce wadda girmansa da darajarsa ta wuce ace yana irin wadannan abubuwan nan idan dai mai kaunar Kano ne shi.

“Don haka muna muku fatan alheri da fatan kowa zai koma gidansa lafiya bisa ziyarar jaddada mubaya’ar su ga gwamnatin ta Kano yau Alhamis.”

A ƙarshe, dubban tsoffin kansillolin wanda suka yi tattaki ɗauke da kwalaye da rubutun barranta kansu da kalaman, sun kewaya cikin sakatariyar Audu Baƙo zuwa ma’aikatar ƙananan hukumomi domin nuna goyon bayansu ga ayyukan alherin gwamnan jihar.

By Babaji