Yanzu-yanzu: Naira miliyan 8.5 ne kafin-alƙalamin hajjin 2026, inji NAHCON

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON) ta ayyana Naira miliyan 8.5 a matsayin kafin-alƙalami na aikin hajjin shekarar 2026 daga yanzu zuwa lokacin da za a cimma matsaya tsakanin hukumomin Saudiyya da Nijeriya kan wasu muhimman al’amuran da suka shafi maniyyata.

NAHCON ta bayyana haka ne a yayin wani zama tsakanin manyan jami’anta da shugabanni da sakatarorin hukumomin jigilar alhazai na jihohi da nufin nazarin aikin hajjin da ya gabata da kuma fara shirin na shekara mai zuwa.

A sanarwar da mataimakiyar daraktan yaɗa labaran hukumar, Fatima Sanda Usara ta fitar, NAHCON ta ce an gabatar da farashin ne domin bai wa masu shirin zuwa hajji a baɗi damar kimtsawa bisa tsari mai kyau.

Ta ce, yayin da aka zaɓi N8.5m a matsayin farashin yanzu, za a bayyana na asalin bayan kammala tattauna batutuwan da suka shafi masauki, ciyarwa, sufuri da wasu muhimman al’amura da hukumomin Saudiyya ke samar wa alhazai.

Haka kuma, a wani karo Nijeriya tana da gurbin kujerun hajji guda 95,000 ga maniyyata a hajjin na 2026.

Sannan, za a raba su ne a tsakanin jihohi 36 na ƙasar da Birnin Tarayya Abuja da kuma jami’an tsaro, kamar yadda aka yi a wanda ya gabata.

Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya yi amfani da damar wajen miƙa godiyarsa ga Shugaba Bola Tinubu bisa gagarumar gudunmuwarsa ga harkokin hukumar da kuma maniyyata a Nijeriya.

By Babaji