Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Hukumar Kiyaye Haɗurra ta ƙasa (FRSC), Corps Marshal Shehu Mohammed, ya ce, bai wa jami’an kiyaye haɗura makamai na iya zama hanya ɗaya tilo da za a iya aiwatar da dokokin hanya yadda ya kamata a kan manyan titunan Nijeriya da ke ƙara taɓarɓarewa.
Yayin da ya ke magana a gidan Talabijin na Arise News a jiya Alhamis, inda Blueprint Manhaja ta sa a kai, shugaban hukumar ta FRSC ya zayyano ƙalubalen da jami’ansa ke fuskanta a lokacin da suke fuskantar manyan motoci da tankokin mai da tireloli masu yawa.
“Yaya za ka tsayar da tirela ko wata tanka a hanya? Yaya ku ke yin haka kawai? Yana da matuƙar wahala da kasada,” inji Mohammed.
“Babbar mota, musamman wacce ke ɗauke da fasinjoji 100 a samanta da dabbobi, kuma kana da ma’aikata huɗu kawai a matsayin tawagar sintiri, ta yaya za ka dakatar da hakan?”
Ya ƙara da cewa, ba tare da isasshen “ikon haɗin kai ba,” ma’aikatan FRSC galibi ana barin su ba tare da wani taimako ba wajen fuskantar manyan laifuka.
“Idan ba ku da ikon tilasta wani abu, babu yadda za ku iya cimma wannan tilastawa,” inji shi.
Mohammed ya kuma yi tsokaci kan zarge-zargen cin hanci da karɓar rashawa da wasu jami’an ke yi a lokuta da dama, lamarin da ke janyo cece-kuce a shafukan sada zumunta.
Ya yarda cewa akwai matsalar amma ya dage cewa hukumar FRSC ta fi yawancin hukumomin ladabtar da ma’aikatan da suka yi kuskure.
“Muna da ƙarin bayanan sallamawa da korar ma’aikatanmu saboda cin hanci da rashawa,” inji shi, tare da lura da cewa Corps na aiwatar da tsauraran matakan aiki don bincikar rashin ɗa’a.
