Abinda ya sa ake buƙatar shawarwarin lafiyar ƙwaƙwalwa a harkokin yau da kullum – Ƙwararre

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wani Farfesan nazarin halayyar ɗan-adam a Jami’ar ‘National Open University of Nigeria’ (NOUN) mai suna Fidel Onjefu Okopi, ya ce shawarwarin lafiyar ƙwaƙwalwa daga ƙwararru abu ne da bai kamata a taƙaice shi a makarantu da ofisoshi ba.

A cewarsa, akwai buƙatar a sanya a shi a matsayin ɓangare na harkokin rayuwar ɗan-adam na yau da kullum.

A wata takarda daga Daraktan yaɗa labaran NOUN, Farfesan, wanda ma’aikaci ne a tsangayar ilimi ta jami’ar ya gabatar da jawabin ne a wata lakca da ya yi a wani ɗakin taro da ke jami’ar a ranar Alhamis.

A lakcar tasa mai taken ‘From Heart to Heart: Integrating Psychosocial Counseling into Daily Life to Build A Harmonious Nigeria’, Okopi ya bayyana cewa ire-iren shawarwarin suna da fa’idodi sosai a harkokin yau da kullum saboda yadda suke tasiri a tunani, alaƙoƙi da fannonin rayuwa.

Ya ce, hakan yana inganta matakin wayewa, ƙarfin fahimta, saurin sabawa da ababe masu amfani, ƙulla alaƙa mai amfani da taimakon wasu wajen sanin ciwon kansu game da al’amuran rayuwar kullum.

Ya ƙara da cewa, ƙarfin bai wa kai shawara mai kyau ba tare da wani ya ɗora ka a kai ba abu ne mai muhimmanci ga ɗan-adam.

Don haka ya yi kira ga al’umma da a riƙa awaitar da shi a mataki na gida, unguwanni da wuraren aiki, lamarin da zai taimaka wajen inganta tunanin al’umma domin ciyar da kansa da al’amuransu gaba.

By Babaji