Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Hukumar yi wa kamfanoni da ƙungiyoyi rijista ta ƙasa (CAC) ta ƙaddamar da sabon dandalin yin rijista ta amfani da fasahar nan ta (AI), domin rage ɓata lokaci da kuma sauƙaƙawa ƴan kasuwa yin rijistar kamfanoni.
Yayin jawabi a taron masu ruwa da tsaki na CAC da aka gudanar a ɗakin taro FABS, da ke Kano.
Babban sakataren hukumar, Barista Hussain Ishaq Magaji, SAN, ya bayyana cewa sabon tsarin—wanda ake kira Intelligent Company Registration Portal (iCRP)—na iya kammala rijistar sunan kasuwanci wato (Business Name) cikin ƙasa da mintuna 10, sannan kuma yin rijistar kamfani mai iyaka da nauyin bashi (limited liability) cikin ƙasa da mintuna 30.
“Wannan ita ce sabuwar Najeriya da muke ginawa,” in ji shi. “Ba tare da sanin wani a CAC ba, ko kuma biyan dillali, za ka iya yi wa kasuwancinka rijista kuma ka samu takardarka kai tsaye cikin ƙasa da mintuna 10.”
Taron na Kano, wanda ya biyo bayan makamancinsa a Legas da Fatakwal, ya haɗa abokan hulɗa da masu amfani da ayyukan hukumar domin tattauna ƙalubale da hanyoyin inganta ayyuka.
Babban sakataren ya ce CAC ta sha fama da tsohon tsarin kwamfuta da ya ƙi ɗaukar bayanai.
Amma bayan watanni kaɗan da zuwansa ofis, cibiyar na karɓar saƙonnin imel sama da 3,000 a kullum, alhali ma’aikata ƙasa da 100 ne ke amsawa. “Wannan rashin adalci ne ga abokan hulɗarmu da kuma ma’aikatarmu,” in ji shi,
yana mai ƙara cewa sabon tsarin AI yanzu yana karanta da kuma ware buƙatun abokan hulɗa cikin minti guda, abin da ya kawar da jinkiri.
An ƙaddamar da tsarin ICRP ne a ranar 30 ga Yuni, 2025, inda yanzu haka yake gudanar da rijistar sunan kasuwanci a matakin farko. An ce sauran sassan rijistar kamfanoni da ƙungiyoyi na ƙarƙashin gwaji kafin a fara amfani da su.
“Babu wata ƙasa da take yin rijistar kasuwanci cikin ƙasa da mintuna 10 a halin yanzu,” in ji babban sakataren, yana mai cewa CAC za ta nuna wannan fasahar a taron Corporate Registers Forum da za a gudanar a Tunisia a watan gobe.
Duk da amincewa da cunkoson aiki da ya gabata, ya tabbatar da cewa ƙarin hanyoyin fasahar AI za su taimaka wajen hanzarta dubawa da amincewar rijista. Ya kuma roƙi mahalarta taron da su bayar da shawarwari domin ƙara inganta ayyukan hukumar.
Shi ma da yake jawabi, shugaban ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA), reshen Ungogo, Barista Ahmed Abubakar, ya yaba da wannan ci gaban, yana mai bayyana shi a matsayin “gagarumin nasara.”
Taron ya samu halartar lauyoyi, masu kasuwanci, wakilan EFCC da ICPC, da kuma sauran jama’a.
