Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Mujaheed A Tijjani shugaban makarantar firamare na Barhim a garin Katsina ya zo na ɗaya a wajan sanin makamar aiki.
Shekarar da ta gabata gwamna Dikko Raɗɗa ya ƙirƙiro da bada kyautar mota ga duk shugaban firamare da ya zo na ɗaya wajen nuna ƙwazo da aikin rubutu.
Shugaban hukumar ilimin bai ɗaya Dr Kabir Magaji wanda ya wakilci gwamnan wajan bikin miƙa motar ga Mujaheed,yayi bayani kan ƙoƙarin da gwamna Raɗɗa ke yi wajen bunƙasa ilimin firamare a jihar.
Ya bayyana cewa malam Mujaheed ya sami nasarar zuwa na ɗaya ne bisa ƙwazo da sadaukar da kai da ya nuna wajen tafiyar da aikin sa.
Dr Magaji ya jawo hankalin malaman firamare a jihar da su ɗauki darasi daga wannan bikin domin ƙara nuna ƙwazo a wajen aikin su.
Ya ce hukumar SUBEB a jihar ta horas da malamai 18,000 tare da ba wasu kyautar TAP domin taimakawa wajen koyarwa.
Haka kuma hukumar ta raba baburan hawa guda 700 a hukumar ilimi na ƙananan hukumomi 34 a jihar domin tabbatar da malamai na zuwa makaranta da kuma sa ido a kan su.
A nasa jawabin sakataren hukumar Dr Isa Zakari ya bayyana Mujaheed cewa yazo na ɗaya ne daga cikin shugabannin firamare 29000 a jihar.
Headmaster Mujaheed ya yi godiya ga Gwamna Dikko Raɗɗa bisa wannan karrama shi da aka yi,ya kuma yabawa Dr Kabir Magaji bisa irin kyawawan shugaban ci da yake nunawa a hukumar musamman wajen ganin harkokin ilmi a jihar sun cigaba.
