‘Yan adawa sun jingine ADA, sun zaɓi ADC yayin da Pantami, El-Rufa’i da wasu suka haɗe da Atiku

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ɓangaren haɗakar ƴan adawa da ke neman karawa da Shugaba Bola Tinubu da jam’iyya mai mulki ta APC a zaɓen 2027, ya zaɓi jam’iyyar ADC a hukumance a matsayin wadda za ta jagoranci fitar da ƴan takararsa sauransu al’amuransu na siyasa

Hakan na nufin ta jingine batun shirin neman yi wa sabuwar jam’iyya mai suna ADA rajista.

An cimma matsayar haka ne yayin da masu ruwa da tsaki suka gudanar da wani zama a Abuja ranar Alhamis, wanda ya samu halartar jiga-jigan ƴan siyasa daga sassan ƙasar daban-daban.

Tsohon shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya jagoranci tawagar, wadda ta ƙunshi Nasir El-Rufai, Isa Pantami, David Mark, Abdulfatai Ahmed, Aminu Tambuwal, Rotimi Amaechi, Rauf Aregbesola, John Odigie-Oyegun, Uche Secondus, Peter Obi, Emeka Ihedioha da kuma Dino Melaye.

A wani saƙo ta X, Atiku ya bayyana zaman nasu a matsayin abinda aka yi domin al’umma da nufin yaƙar halin tsadar rayuwa da al’umma suke fama da ita a ƙasar.

Tsohon shugaban ƙasar ya bayyana cewa an samar da haɗakar ne domin ƙalubalantar yunwa, rashin tsaro da mamaye fannin tattalin siyasar ƙasar daga masu hannu da shuni.

Sakataren haɗakar na ƙasa, Bolaji Abdullahi ya ce a yanzu ƴan ɓangaren adawar sun dakatar da shirin kafa sabuwar jam’iyyar ta ADA.

By Babaji