
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta nanata cewa baki ɗaya kwalejojin fasaha da ke faɗin Nijeriya tana ɗaukar nauyin dukkan abinda ya shafi dawainiyarsu, inda ta gargaɗi jagororinsu da su kauce wa ƙaƙaba wa ɗalibai kuɗaɗen lamuran karatunsu ba bisa ƙa’ida ba.
A sanarwar da Daraktan yaɗa labarai ta Karamin Ministan Ilimi, Maruf Tunji Alausa, wato Folasade Boriowo ta fitar, Ministan ya ce karatun makarantun na FTCs kyauta ne, kamar yadda gwamnati ke ɗaukar nauyin baki ɗaya kashe-kashen da ake yi acikinsu.
A cewarsa, gwamnati tana biyan dukkan buƙatun ɗalibai da suka haɗa da wuraren kwana, inifom, litattafan rubutu, litattafan karatu, takardun bayanan ɗalibai da makaranta, katin shaida, magani da dai suaran su.
Ministan ya yi gargaɗin cewa, babu wani shugaban makaranta, malami ko wani jagoran makaranta da ya isa ya nemi wani kuɗi ba a hukumance ba daga iyayen yara ko wakilansu.
Don haka ya umarci a rubuta takarda ta bai-ɗaya zuwa ga dukkan kwalejojin mai ɗauke da rubutun ‘no-charge policy’ domin faɗakar da ɗalibai da malamai.
Kazalika, ya kirayi iyaye da su ruwaito dukkanin wani rahoto na kuɗi da aka nema daga gare su ba bisa doka ba ga Ma’aikatar Ilimi kai-tsaye ta lambobi kamar haka: 0803 657 6733, 0803 637 3796 ko adireshin Imel, wato [email protected].
