Ɗaliban Kuriga sun shaƙi iskar ‘yanci

Daga BASHIR ISAH

Bayanai daga Jihar Kaduna na nuni da cewa, ɗaliban firamaren da aka yi garkuwa da su kwanan baya a yankin Kuriga a jihar, sun shaƙi iskar ‘yanci.

Gwamnan Jihar, Sanata Uba Sani, shi ne ya ba da sanarwar hakan a shafinsa na Facebook ranar Asabar da tsakar dare

Idan za a iya tunawa, MANHAJA ta rawaito a ranar 8 ga Maris wasu ‘yan bindiga suka kai hari yankin Kuriga, cikin Ƙaramar Hukumar Chilun a jihar Kaduna, inda suka yi awon gaba da yara sama da 200.

Sai dai Gwamnan bai yi wani cikakken bayani kan sako yaran ba.

Sai dai, an ji shi ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro, Mallam Nuhu Ribadu da kuma Rundunar Sojojin Nijeriya.

Idan dai ba a manta ba, kwanan nan aka ji Ministan Tsaro, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, ya furta cewa za a ceto yaran da lamarin ya shaf ba da daɗewa ba.