EFCC ta ƙwato wa ’yan fanshon Kano gidajen Kwankwasiyya da tsofaffin gwamnoni suka sayar

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati, EFCC, ta shiyyar Abuja, ta miqa takardun gidaje 324 da aka ƙwato na ’yan fansho na Jihar Kano ga waɗanda abin ya shafa.

Wannan cigaban dai ya biyo bayan wani bincike da hukumar EFCC ta gudanar kan wani asusun fansho na Naira Biliyan 4.1 da gwamnatocin Jihar Kano da suka shuɗe guda biyu suka hana ’yan fansho.

Binciken Hukumar EFCC ya biyo bayan koke da wata qungiya mai suna “Concerned Kano State Workers and Pensioners” ta shigar a kan zargin karkatar da kuɗaɗen ’yan fansho a jihar.

Kakakin hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa, Mista Dele Oyewale, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

Ya ƙara da cewa, an mika kadarorin ga waɗanda abin ya shafa ne biyo bayan umarnin kwato su na ƙarshe da mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya bayar.

Oyewale ya ci gaba da cewa, “Binciken da hukumar EFCC ta gudanar ya nuna cewa gwamnatin jihar ta ƙulla yarjejeniya da asusun fansho na Jihar Kano na kashi uku na gina gidaje a kan jimillar kuɗi naira biliyan 41, wanda asusun fansho zai ba da gudunmawar Naira Biliyan 4.1.

“Sai dai an yi amfani da gudunmawar da ’yan fansho suka bayar wajen gina gidajen a wasu wurare guda uku da ke cikin garin Kano, Sheikh Ja’afar Mahmud Adam Bandirawo, birnin Sheikh Nasiru Kabara (Amana) da kuma birnin Sheikh Khalifa Ishaq Rabiu, duk a Jihar Kano, inda wasu tsoffin gwamnoni biyu na jihar suka sayar da gidajen ga ’yan uwansu da abokan arziki, wanda hakan ya sa ’yan fanshon suka samu ƙarancin kasafin kuɗi da kuma gidajen da ba su kammala ba.

“Hukumar EFCC ta shiga kuma bayan kammala binciken, ta shigar da aara tare da samun odar ƙarshe na ƙwace kadarorin 324 ga amintattun asusun fansho na Jihar Kano.