Gidauniyar Ɗangote ta ƙaddamar da tallafin kayan abinci a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci ƙaddamar da rabon tallafin kayan abinci da Gidauniniyar Dangote za ta raba wa al’ummar Nijeriya domin rage musu raɗaɗin rayuwa da suke fuskanta.

Da yake ƙaddamar da rabon tallafin a gidan Gwamnatin Kano a ranar Asabar, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga kwamitin da za su gudanar da rabon kayan abincin su zamo masu gaskiya da riƙon amana, tare da tabbatar da tallafin ya isa ga mabuƙatan da aka tanadi abincin domin su.

Yusuf ya kuma ce tuni tallafin kayan abincin ya isa ga ƙananan hukumomin Kano 44.

“Mun gamsu bisa tsarin da gidauniyar ta Ɗangote ta yi na shigar da dakarun Hukumar Hisbah cikin tsarin rabon tallafin abincin; Muna fatan cewa za su tsaya kan adalci da gaskiya yayin gudanar da rabon kayan abincin,” in ji Gwamnan.

Da yake gabatar da tallafin, Alhaji Aliko Ɗangote, ya ce mutane miliyan ɗaya ne za su amafana da tallafin buhunan shinkafa da Gero guda goma-goma daga dukkanin jihohin ƙasar nan.

Gwamnan Kano ya kuma godewa Ɗangote bisa samar da wannan tallafi, musamman a wannan yanayi na tsadar rayuwa da ake fuskanta, tare da yin kira ga mawadata su yi koyi da irin wannan abin alkhairi, domin samun gwaggwaɓan lada a wajen Ubangiji S.W.T.

A nata Jawabin, Babbar manajanar daraktan kasuwancin Kamfanin Ɗangote Hajiya Fatima Aliko Ɗangote, ta ce ganin irin yadda Nijeriya ke cikin halin yunwa, hakan ya sa suka yi hanzari don a ga an tallafa wa mutane don su samu su ci abinci.

“Yau muka fara rabawa a nan Kano, amma a Nijeriya gaba ɗaya da muke da ƙananan hukumomi 774 za a raba wannan shinkafa sama da buhu miliyan ɗaya.

“Kano da yake ita ce gidanmu, kuma jiha ce da take da al’umma da yawa, wannan ya sa muka ga lallai ya kamata mu fara da gida, don haka a nan Kano za a raba shinkafa buhu 120,000 daga nan kuma za a motsa a tafi sauran jahohin ƙasar nan”. Inji Hajiya Fatima Dangote