‘Yan bindiga sun kashe masu Sallar Tarawihi a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Waɗansu ‘yan bindiga dauke da makamai sun yi dirar mikiya a ƙauyen Mai ruwa dake cikin karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina, inda suka nufi gidan wani babban ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa mai suna Alhaji Lado Mai ruwa, suka harbe shi tare da wani makocinsa har lahira daga bisani suka sace iyalinsa.

Lamarin ya faru a ranar Asabar da dare lokacin da marigayan tsaka da Sallar Tarawihi.

Ɗaya daga cikin ‘ya ‘yan marigayin ya tabbatar da kashe mahaifin na su tare da wani maƙwabcinsa Sani Autan Haris.

Rahotanni da jaridar Manhaja ta samu sun bayyana cewar, varayin sun hallaka Alhaji Lado nan take bayan da ya ƙi amince wa ya bi su zuwa daji, dama ana ganin sun shigo ƙauyen ne saboda su tafi da shi.

Daga bisani ɓarayin sun shiga gidan shi, inda suka yi nasarar sace ‘ya’yan marigayin mata su biyu gami da matarsa.

Wannan harin ba shi bane karon farko da ‘yan bindiga ke shiga Masallaci su sace masallata lokacin da ake gudanar da sallar tarawihi, domin kuwa ko da a shekarar da ta gabata a ƙarshen watan mayu, shekarar 2023 sai da ɓarayin suka kai wa wasu masu Sallar tarawihi hari, a ƙaramar hukumar Jibiya tare da yin awon gaba da mutane fiye da ashirin (20) a farmakin.