Yadda sabbin gwamnoni 13 suka kinkimi bashin N226.8bn a cikin wata shida – DMO

Daga BASHIR ISAH

Bayabnan da Manhaja ta tattaron sun ce, a jimilIance wasu sabbin gwamnoni su 13 sun ci bashi da ya kai Naira Biliyan 226.8 a cikin watanni shida da suka yi a ofis.

Wannan bashin kuwa ya shafi wanda gwamnonin suka ci a gida da kuma ƙetare.

Binciken News Point Nigeria ya gano cewa, wasu gwamnonin jihohi 16 kuma, basussukan da suka ciyo ya ƙaruwa da Naira Biliyan 509.3.

An yi lissafin basussukan ƙetaren ne kan lissafin N889 kan $1 kamar yadda Ofishin Kula da Basussuka (DMO) ya nuna.

Rahoton DMO ya ce an tattaro bayanan basussukan ne daga gida da ƙetare, kamar Bankin Duniya da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) da sauransu.

Jihohin da lamarin ya shafa sun haɗa da Benue, Cross Rivers, Katsina, Niger, Plateau, Rivers, Zamfara da kuma Birnin Tarayya wanda jimillar bashin da suka kinkimo a vikin gida ya kai Naira Biliyan 115.57.

Yayin da gwamnonin Ebonyi, Kaduna, Kano, Niger, Plateau, Sokoto, Taraba da Zamfara, suka ciyo bashin Dala Miliyan 125.1 (kwatankwacin N111.24bn) daga ƙetare.

Rahoton ya ce Gwamna Bassey Otu na Jihar Cross River, shi ne kan gaba, inda bashin da ya ci a gida ya kai N16.2bn na ƙetare $57.95m daga Yuni zuwa Disamban 2023.

Sai kuma Jihar Katsina da ta rufa masa baya inda bashin N36.93bn, wato bashin da ake bin ta ya ƙaru daga N62.37bn zuwa N99.3bn ya zuwa Disamban 2023.

Gaba sai Jihar Niger, wadda ta ci bashin N17.85bn, wato bashinta ya ƙaru daga N121.95bn a Yunin 2023 zuwa N139.8bn a Disambann 2023.

Jihar Plateau ita ce ta huɗu, wanda bashin da ake bin ta ya kai N16.32bn; sai Rivers mai N7.07bn; Zamfara, N14.26bn da kuma FCT mai N6.75bn.

A ɓangaren basussukan ƙetare kuwa, rahoton ya ce Gwamna Francis Nwifuru na Jihar Ebonyi ta kinkimi bashin $37.54m, sai kuma Gwamna Uba Sani na Kaduna $17.69m.

Haka nan, Kano ta ari $6.6m; Niger $1.27m; Plateau $831,008; Sokoto $499,472; Taraba $1.51m; sannan Zamfara $655,563.