An karrama Janar Gusau da lambar NIPR

Daga BASHIR ISAH

A ranar Larabar da ta gabata aka karrama Muƙaddashin Darakta na Sashen Labarai na Tsaro, Brigadier General Ismaila Gusau, Ph.D. mni, da lambar yabo ta NIPR.

Cibiyar Hulɗa da Jama’a ta Ƙasa ita ce ta karrama jami’in da wannan lamba ta yabo.

An karrama Gusau ne saboda hazaƙarsa wajen ƙoƙarin sauke nauyin aiki da ya rataya a wuyansa.

Kuma an karrama shi ne tare da wasu a wajen taron wanda cibiyar da ta ɗauki nauyin shiryawa ta saba shiryawa duk shekara.

‘Yan jaridu da jami’an hulɗa da jama’a daga sassa daban-daban na daga cikin waɗanda cibiyar ta karrama a wajen taron da ya gudana a Abuja.

Kafin wannan lokaci, Janar Gusau ya samu karramawa da lambobin yabo a gida da ƙetare saboda ƙwazo da kuma ƙwarewarsa.