Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ziyarar aiki ta tarihi da Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya kai ƙasar Birtaniya ta kai ƙololuwa a ranar Laraba, yayin da shi da Sarkin Birtaniya, King Charles III, suka gabatar da muhimman jawabai a wata babbar liyafar gwamnati da aka shirya a Fadar Windsor da ke Ingila, inda sarkin ya bayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ba ƙashin yarwa ba.
Rahotanni sun nuna cewa taron, wanda ya samu halartar manyan ‘yan gidan sarauta ciki har da Sarauniya Camilla da Yarima William tare da Catherine, Yariman Wales, ya sake jaddada dangantaka mai ƙarfi da tarihi tsakanin Nijeriya da Birtaniya.
A jawabinsa, Sarki Charles ya yi maraba da Shugaba Tinubu da uwargidansa, Oluremi Tinubu, inda ya yaba da irin ci gaban da Nijeriya ke samu da kuma tasirinta a duniya.
Ya bayyana Nijeriya a matsayin ƙasa mai cike da kuzari da matasa, wadda ke da rawar gani wajen tunkarar manyan ƙalubalen duniya.
“Nijeriya ba wai kawai ta canja ba ce, ta kai matsayin da ake alfahari da ita, wacce ba ƙashin yarwa ba ce” inji Sarkin, yana mai nuna cewa yawan jama’ar ƙasar da ya haura miliyan 230 na daga cikin ginshiƙan ƙarfinta.
Ya kuma yaba da gudunmawar ‘yan Nijeriya da ke zaune a Birtaniya, yana mai bayyana su a matsayin gada mai rai da ke haɗa ƙasashen biyu, musamman a fannoni kamar lafiya, kasuwanci, ilimi, wasanni da fasaha. Haka kuma ya yi ishara da tasirin al’adun Nijeriya, daga kiɗan Afrobeats zuwa fina-finan Nollywood da kuma ƙwallon ƙafa na Premier League.
A ɓangaren tattalin arziki, ya jaddada cewa dangantakar kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu na ƙara ƙarfi, inda Nijeriya ta zama babbar kasuwar fitar da kaya ta Birtaniya a Afirka. Ya kuma ambaci haɓakar haɗin gwiwa a ilimi da fasaha a matsayin wata alama ta ci gaba.
Sai dai Sarkin ya amince cewa tarihin dangantakar ƙasashen biyu ya ƙunshi wasu abubuwa masu zafi, amma ya jaddada muhimmancin koyo daga baya domin gina makoma mai cike da mutunta juna da haɗin kai.
A nasa jawabin, Shugaba Tinubu ya bayyana wannan liyafa a matsayin babban abin girmamawa, yana mai cewa shi ne shugaban Nijeriya na farko da ya yi jawabi a irin wannan taro a Windsor.
Ya yaba wa rawar da Birtaniya ta taka wajen gina tsarin dimokuraɗiyya, yana mai ambaton dokar Magna Carta da kuma tunanin manyan masu falsafa da suka yi tasiri a tsarin siyasa a duniya.
Tinubu ya kuma jaddada muhimmancin ‘yan Nijeriya mazauna Birtaniya, yana mai cewa suna daga cikin al’ummomin da suka fi tasiri a duniya.
Ya ambaci fitattun ‘yan wasa masu asalin Nijeriya kamar Bukayo Saka da Anthony Joshua a matsayin misalan alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu.
Dangane da tsaro, shugaban ya bayyana rawar da Nijeriya ke takawa wajen yaƙi da ta’addanci a yankin Sahel, yana mai kira ga ƙarin haɗin gwiwa da Birtaniya. Ya kuma bayyana shirin ganawa da Firayim Ministan Birtaniya, Keir Starmer, domin ƙarfafa alaƙar tsaro.
A wani ɓangare mai taɓa zuciya, Tinubu ya gode wa Birtaniya bisa ba shi mafaka a lokacin mulkin soja a Nijeriya, yana mai cewa wannan alheri ba zai taɓa mantuwa ba.
Dukkan bangarorin biyu sun jaddada muhimmancin ƙungiyar Commonwealth of Nations a matsayin dandali na haɗin kai, tare da kira ga ƙarfafa kasuwanci, daidaita dokoki da bunƙasa tattalin arziki.
An rufe taron da fatan alheri gabanin bikin Eid al-Fitr, inda Sarki Charles ya ɗaga kofin yabo ga Nijeriya da kalmar, “Ba a bar Nijeriya a baya ba,” yayin da Shugaba Tinubu ya yaba da ɗorewar zumunci tsakanin ƙasashen biyu.
Ziyarar ta zama wata muhimmiyar alama a dangantakar Nijeriya da Birtaniya, tana ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa a fannoni daban-daban da suka haɗa da diflomasiyya, kasuwanci, al’adu da tsaro a wannan zamani na haɗin duniya.
