Me zai iya biyo bayan ƙaurace wa taron APC da sanatocin Kebbi suka yi?

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi 

Sanatoci uku da suka yi gudun hijira, don neman mafaka da matsayi a Jam’iyyar PDP bayan da Jam’iyyar APC ta fatattake su a fakaice kafin babban zaɓen da ya gabata a shekarar 2023, waɗanda kuma bayan PDP ta karɓe su hannu biyu, inda ta ba su takara kuma suka ci zaɓe, sannan suka sake dawo wa APC, sun ƙaurace wa taron zaɓen shugabannin jam’iyyar na jiha da aka gudanar a Birnin Kebbi, babban birnin jihar, ranar Talatar makon jiya.

Sanatocin dai sun haɗa da Adamu Aliero mai wakiltar Kebbi ta Tsakiya, Yahaya Abdullahi mai wakiltar Kebbi ta Arewa da kuma Garba Maidoki mai wakiltar Kebbi ta Kudu.

Waɗansu majiyoyi sun shaida wa wakilin Blueprint Manhaja cewa, sanatocin ba su halarci taron ba haka kuma ba a ga magoya bayansu a wajen taron ba.

Majiyoyi na kusa da sanatocin sun bayyana cewa, tun daga matakin mazaɓu har zuwa ƙananan hukumomi ba a bai wa magoya bayansu damar samun muƙamai ko ɗaya ba, duk da cewa, an ce an cimma yarjejeniya kafin su sauya sheƙa zuwa APC.

Har wa yau dai bayanai daga majiyoyi daban-daban sun nuna cewa, sanatocin sun ƙaurace wa taron Jam’iyyar ne, saboda su nuna rashin jin daɗinsu da kuma ƙin amincewarsu da taron, wanda suka ce an shirya shi ne bisa ga son rai na waɗansu ’yan tsirarrun mutane, saboda cimma biyan wata buƙata ta ƙashin kansu.

Bisa ga sanin hali da kuma tarihin siyasar jihar Kebbi ko kuma Nijeriya bakiɗaya, canja sheka ko yin ko oho ko kuma ungulu da kan zabo lokacin zaɓe, musamman masu tunani irin na idan ban samu ba, to kowa ma ya rasa a wajen ɗan siyasa bisa ga rashin cimma muradinsa a wata jam’iyya, ba wani abin mamaki ko kunya ba ne ya sanya raɗe-raɗin yiyuwar ɗaukar matakin da waɗanda ke ganin ba a yi musu daidai ba ya ya sanya shakkar kasancewar ɓangaren da ke ganin an mayar da su ’ya’yan mowa a zukatan ’yan siyasa a jihar.

Kamar dai yadda aka saba idan lokacin raba muƙaman siyasa ya zo akan yi wani tsari ne na kowane jigo daga cikin ’yan siyasa ya kawo nasa mutanen, saboda a yi raba daidai, domin tunanin a gudu tare a tsira tare, amma sai ga shi a wannan karon wani ɓangare ne ya mamaye kusan dukkan kujerin siyasa a jihar.

Wani daga cikin magoya bayan ɓangaren Sanata Adamu Aliero na gundumar Kebbi ta Tsakiya da ke ƙawance da Sanata Yahaya Abdullahi na gundumar Kebbi ta Arewa tare da Sanata Musa Maidoki na gundumar Kebbi ta Kudu, wanda bai so a bayyana sunansa ba, ya bayyana wa wakilin Blueprint Manhaja a jihar Kebbi da cewa, “maganar gaskiya wannan wani tsari ne aka bijiro da shi da Bahaushe ke kira ‘kora da hali’, saboda sanin kowa ne a duk lokacin da za a yi irin wannan akan zauna ne a kan tebur a yi tsari mai tsafta wanda za a tafi tare da kowa, amma yanzu sai ga shi waɗansu mutane ne suka shiga ɗaki suka shirya yadda suke so suka fito suka gaya wa duniya wai an yi zaɓen shugabanni hasali ma waɗannan sanatocin ba su da labarin wannan tsarin, wannan shine ya sanya su kuma da magoya bayansu suka ƙaurace wa taron.”

Ya ƙara da cewa, da ya ke iyayen gidansu mutane ne masu biyayya ga tsarin jam’iyya a dalilin haka suka zauna suka shirya korafi suka kuma gabatar da shi a gaban jam’iyya ta ƙasa, don dubawa tare da ɗaukar matakin da ya dace wanda kuma rashin yi musu adalci yana iya sanya su ɗaukar matakin da ya dace da su.

A ɗaya bangaren kuma wani daga cikin magoya bayan Sanata Atiku Bagudu, Alhaji Aliyu ya bayyana cewa, su a wajen su an yi zaɓen shugabanni bisa ƙa’ida da dokokin Jam’iyyar APC bisa ga tsarin da ya dace, saboda an raba muƙamai kuma kowace ƙaramar hukumar mulki ta samu.

Bisa ga tsari na siyasa duk inda gwamna ya ke shi ne ke da alhaki na jagorancin jam’iyya saboda haka ba zai yiyu wadansu yan tsirarrun mutane su koma gefe su ja daga ba su nuna sai an yi yadda suke ba. Wanda ke ganin ba a yi masa daidai ba yana da hurumin yin korafi amma ba lallai ba ne ta canja ba. 

Ya bayyana cewa sashe na 83(5) da (6) na kundin dokar zaɓe ta 2026 ya haramta ma kotuna tsoma baki ko karɓar ƙararrakin da su ka shafi harkoki ko al’amuran cikin gida na jam’iyyu, tare da ƙarfafa ikon cikin gida na jam’iyya na ƙashin kanta. Wannan yana nuna cewa duk wani son zuciya da a ka aiwatar a cikin jam’iyya ba ka da hurumin da za ka kai ƙara kotu, idan kuma ka sake ka kai to ciko ne zai biyo gyartai, saboda za a ci ka tarar kuɗi Naira Miliyan 10 kai da ka kai ƙarar, haka shi ma lauyan da ya shigar da ƙarar zai biya tarar kuɗi Naira Miliyan 10 domin kuwa dukansu sun aikata laifi.

Ana hasashen wannan damar ce a ke son a yi amfani da ita don cimma biyan buƙatun waɗansu mutane wanda wannan tsari da aka shigo da shi ba ƙaramin ƙara lalata dimukraɗiyyar cikin gidan jam’iyyun siyasa zai yi ba, kuma zai haifar da matsalolin cikin gida na jam’iyyun siyasa da dama.

Idan za a iya tunawa, a cikin wannan sabon kundin zaɓen dai an soke tsarin ‘delegate’ wurin zaɓen fidda gwani, da a ka soke shi kuma sai a ka ce an haramta ma kowa shigar da ƙara a kan duk wata matsala ta cikin gida, kenan za a iya yi wa waɗansu ba daidai ba wurin fitar da ɗan takara sannan kuma ba ka da ikon zuwa kotu, wannan shi ne an dake ka kuma an hana ka kuka.

Alhaji Dan Ayya Sahabi yi ya bayyana cewa, daga cikin irin matsalolin da za a samu sakamakon hana kotuna sanya baki a harkar cikin gida sun haɗa da danniya ga haƙƙokan yayan jam’iyya dan shugabannin jam’iyya suka nuna son zuciya ko rashin gaskiya, mambobi ba su da wata kafa ta doka da za su iya ƙalubalantar wannan rashin gaskiyar sanadiyyar toshe masu hanyar zuwa kotu.

Kuma rashin adalci yana iya sanya mambobi su riƙa yi wa jam’iyya zagon ƙasa ko kuma su fice su koma wadansu jam’iyyun, wanda hakan zai iya raunana tsarin dimukraɗiyya.

Haka zalika yana haifar da fargabar cewa idan talakawa suka ga ana ƙaƙaba masu ‘yan takara ba tare da bin ƙa’ida ba, hakan zai sa su daina fitowa zaɓe.

Duk da ya ke wannan wata hanya ce ta saukaka wa hukumar zabe wadansu wahalhalu ne musamman abinda ya shafi bayarda shaida a kotu sai dai akwai barazanar rashin samarda wata takamaimiyar hanyar da za a tabbatar da cewa shugabannin jam’iyya ba su yi amfani da wannan damar wajen murƙushe ra’ayin mambobinsu ba.

Yanzu dai waɗannan da ke ganin an mayar da su ’ya’yan Mowa sun kai ƙorafi sama kuma su da magoya bayansu sun yi gum suna kan jiran yadda za ta kaya.

By ukarofi