2027: Al’ummar JIhar Taraba sun yi kira ga Jaji Sambo da ya fito takarar Gwamna

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A yayin da saura wata goma sha huɗu a shiga shekarar 2027, tuni matasa daga sassa daban-daban da ke Jihar Taraba suka fara kiraye-kiraye ga tsohon babban Ministan Sufuri na zamanin mulkin marigayi tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wato Mu’azu Jaji Sambo da ya fito ya nemi kujerar Gwamna. 

A sanarwar da ƙungiyoyi daban-daban suka fitar sun nuna matuƙar gamsuwa da nagartar tsohon Ministan, inda suka jaddada wajabcin mara masa baya a zaɓe mai zuwa domin ciyar da jihar Taraba gaba.

Da yake magana a wani taron da suka gudanar a Jalingo, ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar matasa daga shiyyar Taraba ta Arewa, Kamaluddeen Bobbo Tafawa, ya ce al’ummar jihar Taraba za su fara sanin daɗin mulkin dimokuraɗiyya idan Allah Ya kawo Mu’azu Jaji Sambo kan karagar kujerar Gwamna.

“Rawar da ya taka kan kujerar Ministan Ayyuka da Gidaje da kuma babban Ministan Sufuri duk da ƙarancin lokaci, ma’auni ne da ke nuna tabbas zai kawo cigaban da al’ummar Taraba suka daɗe suna muradi,” a cewar Tafawa. 

Shi kuma a nasa ɓangaren, Jauro Rufai Maphindi ya wallafa buɗaɗɗiyar wasiƙa a shafinsa na Facebook ne zuwa ga Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, inda yake bayyana muhimmancin tsayar da Mu’azu Jaji Sambo a matsayin ɗan takarar Gwamna a zaɓe mai zuwa.

Wasiƙar wanda ta samu yaɗuwa sosai a kofofin sada zumunta, ya ƙunshi manyan ayyukan alkhairi da Mu’azu Jaji Sambo ya aiwatar cikin watanni goma sha bakwai da ya yi a matsayin minista. Ayyukan sun ƙunshi sabbin tituna a fadar gwamnatin Taraba, samar da ayyukan yi ga dinbin matasa da kuma tallafawa marayu da gajiyayyu a ciki da wajen jihar Taraba. 

“Ita gaskiya bata neman ado. Don Allah ku yi wa bawan Allah nan addu’a Allah ya cika mishi burinsa na duniya da lahira.” Cewar Abdulrazak Ibrahim, wanda ya wallafa hakan a shafinsa na sada zumunta (Facebook) domin nuna goyon bayansa ga kiran da ake yiwa Mu’azu Jaji Sambo.

Da yake zantawa da wakilinmu, wani matashi mai suna Saeed Saeed Jauro yace suna nan suna ta shirye-shirye gayyato sama da matasa dubu daya a shiyyar Taraba ta tsakiya domin nuna goyon baya ga kiraye-kiraye da ake yiwa tsohon ministan.

Shi kuma Saddam A. Danladi, wanda daya ne daga cikin daruruwan matasa da ke yi wa Tsohon Ministan Sufuri Mu’azu Jaji Sambo kiraye-kiraye a kafofin sada zumunta daga ƙaramar hukumar Karim Lamido, ya bayyana cewa suna haɗa shi da Allah ya taimaka ya amsa kiransu.

A nasa ɓangaren, Malam Hamman Adama Mijinyawa ya ce tsohon minista Mu’azu Jaji Sambo mutum ne mai gaskiya, rikon amana, da son cigaban ƙasa. Inda ya bayyana cewa duk da matsayin da Allah ya ba shi na kujerar Minista ba manta da tsoffin abokai ba, saboda haka zai samu duk goyon bayan da yake buƙata daga garesu idan har Allah yasa ya amince ya amsa kiran da talakawa ke masa

A halin yanzu dai Tsohon Ministan bai bayyana zai tsaya takara ko a’a, amma alamu sun nuna kullum yana samun karɓuwa musamman a tsakanin matasan jihar Taraba.

By ukarofi