Daga WAKILINMU
Aallah Ya yi wa tsohon ɗan siyasa Sanata Arthur Nzeribe rasuwa.
Wata majiya ta kusa da ahalin marigayin wadda ta buƙaci a sakaya sunanta, ita ce ta tabbatar da labarin rasuwar, inda ta ce ya rasu ne da yammacin ranar Asabar.
Nzeribe, wanda ya kasance ɗaya daga cikin ‘yan siyasar jamhuriya ta fako, ya wakilci shiyyar Imo ta yamma a Majalisar Tarayya.
Bayanai sun nuna marigayin wanda ɗan asalin Jihar Imo ne, ya kasance sanata mafi daɗewa a kan kujerar sanata a tarihin siyasar Nijeriya.
An haifi marigayin ne a ranar 2 ga Nuwamban 1938, inda ya bar duniya yana da shekara 84.
