Deborah: Yadda aka kai waɗanda ake zargi da kisan ɗalibar kurkuku

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wata kotun majistire da ke Sakkwato ta tura mutanen nan biyu da aka kama da ake tuhuma dangane da kisan ɗaliba Deborah Samuel gidan gyarar hali.

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ce ta kama matasan biyu ranar Alhamis 12 ga watan Mayu, a lokacin da ɗalibai suka kashe Deborah Samuel kuma suka ƙona ta akan zargin ta yi ɓatanci ga fiyayyen halitta.

A ranar Litinin 16 ga Mayu ce aka gurfanar da matasan biyu: Bilyaminu Aliyu da Aminu Hukunci, waɗanda ɗalibai ne a kwalejin koyar da malanta ta Shehu Shagari.

Sai dai bayan da aka karanta musu laifin da ake tuhumarsu wanda ya yi sanadin salwantar rayuwar Deborah sun qi aminta da laifin, abinda ya sa ɗan sanda mai gabatar da ƙara, Sufeto Khalil Musa, ya nemi kotun da ta ƙara basu lokaci domin faɗaɗawa da kammala bincikensu.

Jagoran lauyoyi dake tsaya wa waɗanda ake tuhuma Farfesa Mansur Ibrahim ya aminta da ƙarin lokacin da ‘yan sandan suka nema, kuma ya shigar da wata buƙata ta neman bayar da belin waɗanda ake tuhuma.

Jagoran lauyoyin ya karanto sashe na 157 da 161 (a’f) da sashe na 164 na dokar aikata manyan laifuka ta jihar Sakkwato, da kuma sashe na 35(5) na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 mai kwaskwarima a zaman hujjojin neman belin.

Kotun dai ta ɗaga shari’ar zuwa wata rana da za a sanar da lauyoyin nan gaba, ta kuma bayar da umurnin a tura waɗanda ake tuhumar gidan gyara hali.

Wannan zaman kotun dai ya na zaman wani ɓangare na alƙawari da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya yi lokacin da ya gana da wakilan Ƙungiyar Kiristoci ta Ƙasa CAN, reshen jihar Sakkwato a ƙarƙashin jagorancin Rev Fr. Nuhu Iliya, inda ya shaida musu cewa za a gudanar da bincike tare da gurfanar da duk wanda aka samu da laifi.

Har wa yau dangane da batun kisan Deborah Samuel, rundunar ‘yan sandan Nijeriya, a wani bayani da ta fitar mai sa hannun kakakinta a Sakkwato, ASP Sanusi Abubakar, ta ƙaryata wani bayani da aka wallafa a yanar gizo na cewa wata ƙwaƙƙwarar majiya ta ‘yan sanda ta ce ɗaya daga cikin waɗanda ake tuhuma da kisan Deborah ba ɗan Nijeriya ba ne, ya shigo ne daga Jamhuriyar Nijar a haramce ya aikata wannan aika-aikar.

Bayanin ya ce rundunar ‘yan sanda ba ta fitar da kowane bayani mai kama da hakan ba, ta ce wasu ne da ke son tunzura jama’a da tayar da fitina suka ƙirƙiri wannan labarin suka wallafa, inda ta buƙaci jama’a da su riqa yaɗa batutuwan da za su kawo zaman lafiya a ƙasa.

Gwamnatin jihar Sakkwato ta sassauta dokar ta baci da ta saka domin daƙile tarzoma da matasa suka soma sanadiyyar kama waɗanda ake tuhuma a kisan Deborah.

By Editor