Mayaƙan IPOB sun ƙone sakatariyar Ƙaramar Hukuma a Anambara

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar ‘yan sandan Jihar Anambara ta tabbatar da ƙona shalkwatar Ƙaramar Hukumar Idemili ta Arewa da ke Ogidi a jihar Anambra a safiyar Litinin.

DSP Tochukwu Ikenga, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ta wayar tarho a Awka.

Ya ce maharan, waɗanda ake zargin mambobin haramtacciyar ƙungiyar IPOB ne, sun kai harin kan shelkwatar Ƙaramar Hukumar da misalin ƙarfe 2 na daren Litinin.

Ikenga ya ƙara da cewa haɗin gwiwa da sauran jami’an tsaro da mutanen gari ne ya sanya a ka samu nasarar fatattakar ‘yan ta’addan.

“Yayin da mu ke magana, har yanzu jami’an tsaro na nan kan lamarin, kuma muna tsare wajen.

“Dole ne in ƙara da cewa al’ummar gari sun taka rawar gani wajen fatattakar ‘yan ta’addan nan, wasu daga cikinsu suka tare da jami’an tsaron su ka fafata da ‘yan ta’addan,”

By Editor