Babu ƙarya Tinubu ya taimaki Buhari-Rarara

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Shuguban ƙungiyar 13×13, kuma babban mawaƙin jam’iyyar APC, Dauda Kahuta Rarara ya bada tabbaci kan furuncin da ɗaya daga cikin masu zawarcin kujerar shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi, wadda wasu ke kallon furucin na sa a matsayin gori ga shugaba Muhammadu Buhari. Rarara ya yi jawabin ne a taron manema labarai da ya kira.

Tinubu ya bayyana muhimmiyar rawar da ya taka a yayin zaɓen shugaba Buhari karo na farko, inda ya yi iƙirarin da ba don shi ba, da bai samu nasarar lashe zaɓen ba.

Rarara dai ya shiga layin waɗanda suka gaskata zancen na jigon jam’iyyar ta APC Bola Ahmad Tinubu, inda ya bayyana yadda abin ya kasance a zaɓen 2015.

“Babu shakka Tinubu ya taimaki Buhari, ko shi kan sa Buharin ba zai musanta hakan ba. Don haka idan ya faɗa, ni ma zan iya maimaitawa domin zancen gaskiya ne.”

Da yake bayar da hujjarsa, mawaƙin ya bayyana yadda suka yi gwagwarmaya a zaɓen 2015, inda a cewarsa Tinubu ne kan gaba, domin shi ya yi ruwa da tsaki har aka kai ga nasarar da ta ɗora Buhari kan karagar mulki.

“Duk wanda yasan yadda aka yi gwagwarmayar yaƙin neman zaɓe na shekarar 2015, to fa ba zai fito ya iya ƙaryata maganar da Tinubu ya yi ba. Kuma duk wanda ka ji ya fito yana ƙaryata hakan to tabbata shi ɗan ‘good evening’ ne, wato daga baya ya zo.

“Ba zan manta ba, a lokacin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ke neman taimako kan sha’anin zaɓensa na farko, a lokacin akwai wani shi ɗan Arewa ne, kuma ya kamata ya taimake shi, amma bai taimake shin ba, sai Bola Ahmad Tinubu ne ya zo ya taimake shi da ƙuri’arshi da kuɗinshi da kuma mutanen shi. inaga wannan ne shi Tinubu yake magana akai, shi ne taimakon da ya ba shi har ya zama ɗan takara a jam’iyyar APC da kuma samun nasarar da ta kai shi ga hawa mulki.”

Rarara ya ƙara da bayyana kan sa a matsayin jigo na jam’iyyar ta APC, kuma masu kishinta, yayin da ya bigi ƙirji ya kira kansa ɗaya daga cikin waɗanda suka bada gudunmuwa a layin biyar na farko a yayin yaƙin neman zaɓe na shugaba Muhammadu Buhari.

Da yake amsa wata tambayar kan yiwuwar yarjejeniya tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari da kuma shi Tinubu kan taimakon da yake iƙirarin ya yi ga shuganan ƙasa, mawaƙin ya ce, “zai iya yiwuwa akwai yarjejeniya ta zan taimake ka a yanzu, idan ka gama sai ka mara min baya, to amma ni ban sani ba ko akwaita, domin lokacin da shi shugaban ƙasa zai nemi taimakon Tinubu akwai yiwar ya amince da duk sharaɗin da zai gindaya masa.”

Mawaƙin ya yi kira ga shugaba Buhari da ya kare martabar Arewa, ta hanyar nuna kyakkyawan misali ga ‘yan Kudu da ke da sha’awar taimaka wa ‘yan takara da suka fito daga Arewa. Inda yake cewa, ko da ba zai taimake shi ba, to kada ya yaƙe shi.

Daga ƙarshe ya yi kira ga shugaban ƙasa da ya dube su, ya aikata ɗaya cikin biyu, ko dai ya taimaki shi Tinubun don biyan bashi, ko kuma ya tabbatar da ya tsaya tsayin daka don ganin an gudanar da sahihin zaɓe, ta hakan ne kawai zai kare mutuncin Arewa wanda zai iya tsawon rai har ɗiya da jikoki.

By Editor