Daga BASHIR ISAH
Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu (Turakin Keffi), ya taya Bola Ahmed Tinubu murnar lashe zaɓen fitar da ɗan takarar da APC ta kammala a ranar Laraba.
Saƙon taya murnar na ƙunshe cikin wasiƙar da Adamun ya aike wa Tinubu a ranar Laraba, musamman don taya shi murna a madadin ɗauakcin mambobin APC.
Adamu ya bayyana nasarar da Tinubun ya samu a matsayin wata alama da ke nuni da cewa lalla,i Jam’iyyar APC ita ce zaɓin kowane ɗan Nijeriya da kuma irin haɗin kan da ake da shi a cikin jam’iyyar.
Ya ce, “Na ji daɗi matuƙa yadda jam’iyyar ta yi magana da murya ɗaya ganin yadda daliget suka yi zaɓe a tsanake suka zaɓe ka a matsayin ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyarmu.
“Ina fata da kuma addu’ar cewa, za mu yi aiki tare don cimma nasara a babban zaɓen 2023 da yardar Allah,” inji Adamu.
Tinubu ya lashe zaɓen fidda gwani na APC ne bayan da ya samu ƙuri’u 1,271 daga cikin ɗaukacin ƙuri’un da aka kaɗa a zaɓen.
