Ɗaliban Kaduna 701 ba za su rubuta jarrabawar WAEC ba

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ɗalibai 701 daga jihar Kaduna ba za su zana jarrabawar kammala sakandire ta WAEC ba saboda rashin ba su damar biyan kuɗaɗen da ya kamata su biya.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa ɗaliban, waɗanda suka fito daga makarantun sakandire daban-daban a jihar an ƙi ba su damar sanya makinsu na makaranta a shafin hukumar da ake shirya jarrabawar kammala karatun sakandiren.

Ko da yake, hukumar daga bisani ta yi kira ga makarantun da abin ya shafa a kan cewa za a ƙara buɗe shafin domin su sanya makin nasu.
Makarantun da abin ya shafi ɗalibansu sun haɗa da Government Secondary School Kuse, wadda ɗalibanta da ke ajin ƙarshe 290 abin ya shafa.

Sai Government Secondary School Independence Way Kaduna, mai ɗalibai 150 da Government Secondary School Kagarko mai ɗalibai 110 da kuma Government Senior Secondary School Iddah mai ɗalibai 100.

Sauran sun haɗar da Al-Bahmeen Academy, Kaduna mai ɗalibai takwas da Kalhyatu AbdulRahman Bin Auf Academy, Jere mai ɗalibai 15 da Great Panaf Schools Kaduna mai ɗalibai 13 da ECWA Secondary School, Kubacha mai ɗalibai 10 sai kuma Government Secondary School Mato mai ɗalibai biyar.

By Editor