Harin Abuja-Kaduna: ‘Yan uwa sun ƙaryata sako waɗanda aka yi garkuwa da su

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

‘Yan uwan fasinjojin da aka yi garkuwa da su a hanyar Abuja zuwa Kaduna sun ƙaryata labarin cewa, an sako musu ‘yan uwa da ke hannun ‘yan bindiga.

Sun ƙaryata labarin ne cikin wata sanarwa da suka fitar ta ƙungiyarsu ta “Relatives of AK9”, ƙarƙashin jagorancin Dokta Abdulfatai Jimoh da Dokta Ba’aba Muhammad.

Sashen sanarwar ya ce, “Labarin sako waɗanda aka yi garkuwa da su a hanyar Abuja-Kaduna wanda aka yaɗa a soshiyal midiya, ba gaskiya ba ne, jama’a su yi watsi da labarin.”

Idan dai ba a manta ba, a ranar 28 ga Maris ɗin da ya gabata ‘yan fashin daji suka kai harin inda suka yi garkuwa da fasinjojin a kusa da Kaduna.

Mutum takwas ne suka mutu sakamakon harin, kana aka yi garkuwa da wasu da dama.

By Editor