Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Kimanin ɗalibai 35,000 ne cibiyar koyon sana’oi da dabarun aiki da aka fi sani da Vocational and Relevant Technology Board a Turance na gwamnatin Jihar Nasarawa da ke Lafiya babbar birnin jihar ta yaye kawo yanzu.
Janar Manajan cibiyar, Dokta Idris Umar Idris ne ya sanar da haka a lokacin da yake zantawa da wakilin mu dangane da harkokin cibiyar a ofishin sa dake cibiyar a Lafiya ranar Litinin, 6 ga Yuni, 2022.
Ya ce cibiyar ta yaye ɗaliban ne daga fannonin karatun ta guda biyu a cibiyar wato fannin koyon sana’o’in da na sanin makamar-aiki ko dabarun aiki.
A cewarsa gwamnatin jihar ta kafa cibiyar ne da manufar samar wa al’ummar jihar musamman matasa ilimin sana’i’o da na dabarun aiki don ba su damar dogara da kansu ba tare da sun dogara ga gwamnati ba.
A cewar Janar Manajan lokacin ya wuce da matasa za su riƙa dogara ga aikin gwamnati ko ga wani shi ya sa gwamnati ta ƙirƙiro da shirin wanda kawo yanzu a cewarsa ta samu ɗimbin nasarori da suka haɗa da yaye ɗalibai dake bada gagaruman gudunmawa a fannonin ayyuka daban-daban a jihar da ƙasa baki ɗaya. Kuma al’ummar jihar na cigaba da yabawa a kullum.
Har ila yau a cewarsa gwamnatin jihar ƙarƙashin shugabancin Gwamna Abdullahi Sule na biyan ɗaliban Naira 5000 kowannensu a kowane ƙarshen wata tare da basu kayayyakin fara aiki bayan sun kammala wa’adin karatunsu na sana’o’in da sauran tallafi don ƙara musu kwarin gwiwa.
Ya kuma bayyana wasu daga cikin kwasa-kwasai da cibiyar ke gudanara cewa sun haɗa da koyon aikin tela da wutar lantarki da gyaran mota da walda da ƙere-ƙere da fannin na’urar kwamfuta na I.C.T da kafinta da sauransu.
Dangane da ƙalubale dake addabar cibiyar a yanzu, Dokta Umar Idris Umar ya bayyana cewa matsalar kawai shine na rashin isheshen ma’aikata.
Ya yaba wa gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule dangane da tallafi da gudunmawa da yake bai wa cibiyar akai-akai don tabbatar da ɗorewa da nasarar harkokin ta, inda ya buƙace shi ya cigaba da haka.
Daga nan sai Janar Manajan ya yi amfani da damar, inda ya yi kira na musamman ga matasa a jihar da ma ƙasa bakiɗaya cewa su yi amfani da damar wajen koyon sana’o’i daban-daban don basu damar dogara da kai kuma kwalliya ta biya kuɗin sabulu ta cimma burin shirin a jihar da ƙasa bakiɗaya.
