Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Hukumar Kula da ayyukan ‘yan sandan Najeriya PSC ta ɗaga muƙamin kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Katsina, CP Bello Shehu zuwa mataimakin sufeto janar na yan sandan Najeriya (Assistant Inspector General Of Police AIG) .
CP Bello Shehu ɗan asalin garin Dukku ne a jihar Gombe, wanda ya shafe kusan shekara ɗaya a matsayin kwamishinan ƴan sanda a jihar Katsina.
