Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kungiyar Mata Masu Kasuwanci da Siyasa (WBP) ta miƙa ta’aziyyarta ga Ministar Harkokin Fasaha, Al’adu, Yawon Buɗe Ido, Hannatu Musawa, bisa rasuwar mahaifiyarta.
ƙungiyar ta bayyana cewa ta karɓi labarin rasuwar marigayiyar cikin matuƙar jimami jim kaɗan bayan da aka yi jana’izarta bisa koyarwar addinin Musulunci.
A cikin wata sanarwa da mai kula da ayyukan ƙungiyar, Hassie Oyama, ta fitar, ƙungiyar ta nuna cikakken goyon baya da jajantawa ga Hannatu Musawa, iyalanta, abokanta da sauran masoyanta a wannan lokaci na baƙin ciki.
Sanarwar ta ce, rasuwar uwa babban rashi ne da ke barin giɓin da ba zai taɓa cika ba, tare da addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa marigayiyar, Ya kuma ba ta Aljannatul Firdausi.
Haka kuma ƙungiyar ta roƙi Allah Ya ba iyalan marigayiyar haƙuri, juriya da ƙarfin guiwar jure wannan babban rashi.
Oyama ta bayyana cewa Hannatu Musawa ta kasance abin koyi ga mata da dama a Nijeriya saboda jajircewarta wajen hidimtawa ƙasa da kuma bayar da gudunmawa ga ci gaban ƙasa.
Ta ce: “A matsayinta na jagora da ta sadaukar da kanta wajen yi wa ƙasa hidima, Hannatu Musawa ta kasance abin alfahari ga mata da dama a Nijeriya. A matsayarmu ta ƙungiyar da ke tallafa wa mata a harkokin jagoranci, kasuwanci da mulki, muna tare da ita a wannan lokaci na jimami tare da miƙa mata da iyalanta ta’aziyya.”
Oyama ta ƙara da cewa rasuwar marigayiyar babban rashi ne ga iyalanta da duk masu kusanci da ita, tare da addu’ar Allah Ya ba su ta’aziyya da nutsuwa.
“Madadin ƙungiyar Mata Masu Kasuwanci da Siyasa ta Nijeriya, ina miƙa saƙon ta’aziyyata ga Hannatu Musawa da iyalanta. Rasuwar uwa na daga cikin mafi girman jarrabawar rayuwa.
“Muna addu’ar Allah Ya jiƙanta da rahama, Ya ba ta hutu na har abada a Aljanna, sannan Ya ba iyalanta ƙarfin hali da juriyar ɗaukar wannan babban rashi. Allah Ya sanya kyawawan abubuwan da ta bari su zama abin tunawa mai daɗi, kuma Ya sa ruhinta ya huta cikin aminci,” inji Oyama.
