Ribadu: Nijeriya ta samar da tsaron bai-ɗaya na kare bututun mai

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da tsararren tsarin aiki da zai jagoranci yadda jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki za su kare kadarorin man fetur, daƙile satar ɗanyen mai da lalata bututun mai, tare da hana tace mai ba bisa ƙa’ida ba.

Mai ba Shugaban ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, ya yi gargaɗin cewa wannan mataki ba zai cimma manufarsa ba sai hukumomin tsaro, kamfanonin mai da ’yan kwangilar tsaro sun tabbatar da cikakken aiwatar da tanade-tanadensa. Ribadu ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Litinin, lokacin da ya ƙaddamar da Tsarin Aiki na Bai-ɗaya (SOP) na tsarin tsaro ga Masana’antar Mai da Iskar Gas ta Nijeriya.

Tsarin zai zama jagora wajen gudanar da sa ido, kama waɗanda ake zargi, tsare su, musayar bayanan sirri da kuma kwashe man fetur da aka ƙwato daga hannun masu aikata laifuka. An tsara wannan tsarin ne domin magance matsalar da ta daɗe tana kawo cikas ga tsaron kadarorin man fetur, inda hukumomin tsaro da dama, hukumomin sa ido, kamfanonin mai da ’yan kwangilar tsaro masu zaman kansu ke gudanar da ayyuka a yankuna iri ɗaya, amma kowannensu na bin nasa ƙa’idoji da nauyin da aka ɗora masa.

A cewar Ribadu, an samar da tsarin ne bayan shawarwari da rundunonin sojoji, hukumomin leƙen asiri, Kamfanin Man Fetur na ƙasa (NNPCL), hukumomin da ke kula da masana’antar, kamfanonin da ke gudanar da ayyukan mai da kuma ’yan kwangilar sa ido na tsaro. Ana sa ran tsarin zai fayyace nauyin da ke kan kowace hukuma, rage saɓani da ruɗani wajen gudanar da ayyukan tsaro, tare da tabbatar da cewa ana bin ƙa’idoji iri ɗaya a duk faɗin masana’antar. Ribadu ya ce, “Tsawon lokaci, satar ɗanyen mai, lalata bututun mai, tace mai ba bisa ƙa’ida ba da sauran laifukan da ke da alaƙa da su sun kasance suna kawo cikas ga samar da mai, lalata muhalli da kuma barazana ga tsaron ƙasa.”

Ya jaddada cewa takardar ba wata ƙa’ida ce ta gudanarwa kawai ba, illa dai wani muhimmin kayan aiki ne da zai inganta haɗin gwiwa, tabbatar da ɗaukar alhaki da kuma kare muhimman ababen more rayuwa na ƙasa. “Amfanin wannan tsarin zai ta’allaka ne kan yadda aka aiwatar da shi,” inji shi.

Saboda haka, ya buƙaci hukumomin tsaro da ’yan kwangilar da abin ya shafa su tabbatar da isar da bayanan tsarin ga shugabannin rundunoni, jami’an da ke bakin aiki da sauran ma’aikatan da za su aiwatar da shi. Haka kuma, Ribadu ya yi kira da a riƙa gudanar da ayyukan tsaro cikin ƙwarewa, musayar bayanan sirri, mutunta ikon kowace hukuma da kuma bin dokokin da ake da su ba tare da kauce musu ba.

Wannan kira na zuwa ne a daidai lokacin da ake tura sojoji, ’yan sanda, jami’an leƙen asiri da ’yan kwangilar tsaro zuwa yankunan da bututun mai ke bi, wuraren haƙo mai da rafuka. Saboda haka, akwai buƙatar a tabbatar da cewa kowa na aiki bisa ƙa’idoji masu inganci, tare da sanin iyakar ikon da doka ta ba shi.

ƙaddamar da sabon tsarin na zuwa ne yayin da Nijeriya ke ci gaba da fuskantar matsalar asarar kuɗaɗen shiga sakamakon satar ɗanyen mai da lalata muhimman kayayyakin more rayuwa. Waɗannan laifuka sun shafi yawan man da ake samarwa, kuɗaɗen shigar gwamnati, al’ummomin da ke zaune a yankunan da ake haƙo mai da kuma muhalli.

By ukarofi

Leave a Reply