Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Kula da Sadarwa ta Nijeriya (NCC) ta fara amfani da sabon tsarin tantance na’urorin sadarwa masu amfani da katin SIM ta hanyar fasahar zamani, domin gano tare da hana jabun wayoyi da sauran na’urorin sadarwa da ba su cika ƙa’idoji ba shiga hanyoyin sadarwar kamfanonin sadarwa a ƙasar.
Daraktan Sashen ƙa’idojin Fasaha da Ingancin Hanyoyin Sadarwa na hukumar, Edoyemi Ogoh, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja, inda ya yi bayani kan matakan da hukumar ke ɗauka domin inganta ƙa’idojin fasaha da tabbatar da ingancin hanyoyin sadarwa. Sabon tsarin ya shafi na’urori da suka haɗa da wayoyin hannu, kwamfutocin hannu (tablets), na’urorin haɗa intanet (modems) da na’urorin karɓar kuɗi ta POS, da sauran na’urorin da ke amfani da katin SIM.
NCC ta ce, manufar wannan mataki ita ce tabbatar da cewa na’urorin sadarwar da ake shigowa da su Nijeriya, sayarwa ko amfani da su sun cika ƙa’idojin fasaha da hukumar ta gindaya. A tsarin kula da harkokin sadarwa, ana kiran wannan tantancewa da Type Approɓal, wato amincewar hukuma ga na’ura bayan an tabbatar da cewa ta cika ƙa’idojin fasaha da ake buƙata kafin a sayar da ita ko a fara amfani da ita a Nijeriya.
Ogoh ya ce sabon tsarin zai ƙara wa hukumar ƙarfin sa ido kan na’urorin da ake shigowa da su ƙasar, waɗanda ake sayarwa a kasuwanni da kuma waɗanda jama’a ke amfani da su. Ya bayyana cewa tsarin zai bai wa hukumar damar tantance na’urori tare da tabbatar da cewa sun samu amincewar NCC, lamarin da zai taimaka wajen inganta ayyukan sadarwa da kuma kare masu amfani daga na’urorin da ba su cika ƙa’idojin da aka gindaya ba. Ya ce, “Mun kuma tabbatar da cewa an shigar da na’urorin da ke cikin hannun masu sayarwa a halin yanzu cikin sabon tsarin yadda ya kamata, sannan duk na’urorin da za a shigo da su Nijeriya daga yanzu za a tantance su tare da tabbatar da sahihancinsu.”
Ya ƙara da cewa, sabon tsarin zai samar da ingantacciyar hanyar gano na’urorin da ba su cika ƙa’idoji ba, waɗanda aka yi wa kwafi ko kuma aka ƙera su na jabu, tare da hana su haɗuwa da hanyoyin sadarwar kamfanonin sadarwa. A cewarsa, ƙaddamar da wannan tsarin ya biyo bayan fitar da ƙa’idojin gudanar da aikin amincewa da na’urorin sadarwa da hukumar ta yi a watan Agustan 2024, da kuma shawarwarin da ta gudanar da masana’antun ƙera na’urori, masu shigo da kaya, ’yan kasuwa, kamfanonin sadarwa, hukumomin gwamnati da ƙungiyoyin da ke da ruwa da tsaki a fannin.
Ya ce NCC ta kuma haɗa kai da Hukumar Kwastom ta Nijeriya da sauran masu ruwa da tsaki a jerin hanyoyin da na’urori ke bi tun daga shigowa da su ƙasar har zuwa lokacin da suka isa hannun masu amfani, domin tabbatar da nasarar aiwatar da sabon tsarin.
