Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira da a sake nazarin Dokar Kula da Haya ta jihar, domin kare masu haya daga ƙarin kuɗin haya ba bisa ƙa’ida ba, musamman na gidaje da shaguna.
Kakakin Majalisar, Isma’il Falgore, ne ya yi wannan kira yayin zaman majalisar, bayan ɗan majalisar da ke wakiltar mazaɓar Takai, Musa Kachako, ya gabatar da ƙuduri kan yadda kuɗin haya ke ƙara tashi a faɗin jihar. Kachako ya bayyana cewa wasu masu gidaje sun ƙara kuɗin hayar shekara daga naira 100,000 zuwa tsakanin naira 200,000 da naira 300,000, yayin da kuɗin hayar shaguna ya tashi daga naira miliyan ɗaya zuwa naira miliyan biyu cikin shekara guda.
Ya ce wannan ƙarin kuɗi na ƙara jefa ’yan kasuwa, manoma da masu ƙaramin ƙarfi cikin matsin tattalin arziki, musamman waɗanda suke dogaro da gidajen haya da wuraren kasuwanci domin gudanar da sana’o’insu da neman abin rayuwa. Sai dai ɗan majalisar ya amince cewa masu gidaje na da ’yancin samun riba mai ma’ana daga jarin da suka zuba. Duk da haka, ya buƙaci samar da ƙa’idojin da za su tabbatar da cewa duk wani ƙarin kuɗin haya ya kasance cikin adalci, tare da hana masu gidaje yin ƙarin kuɗi kwatsam ba tare da sanar da masu haya tun da wuri ba. A cewarsa, sake duba dokar da ake da ita zai taimaka wajen kare haƙƙin masu haya tare da samar da kyakkyawar fahimtar juna tsakanin masu gidaje da waɗanda suke haya.
Wannan kira na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan tashin farashin gidajen haya da shagunan kasuwanci, lamarin da ke ƙara ɗora wa mazauna Jihar Kano da ƙananan ’yan kasuwa nauyin kuɗaɗen gudanar da rayuwa da sana’o’insu.
