Yadda tsohon kakakin ’yan sanda buɗe sabin babin rayuwa a aikin lauya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan Sandan Nijeriya kuma tsohon kakakin rundunar na ƙasa, Frank Mba, ya bayyana dalilin da ya sa ya zaɓi kafa kamfanin lauyoyi bayan ritayarsa daga aikin ’yan sanda, inda ya ce yana kallon matakin a matsayin wata dama ta ci gaba da yi wa al’umma hidima ta wata hanya daban.

Mba ya bayyana hakan ne yayin bikin buɗe kamfaninsa mai suna Frank Mba Legal, da ke Wuse 2 a Abuja, ranar Juma’a, 9 ga Oktoba, 2026, wanda ya zo daidai da bikin zagayowar ranar haihuwarsa.

A cewar wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a ranar Litinin, taron ya samu halartar manyan baƙi, ciki har da Ministar Harkokin Waje, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu; tsofaffin Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Mohammed Abubakar da Usman Baba; da tsofaffin Mataimakan Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Sadiƙ Abubakar, Tijani Baba da Dan Kwara, tare da manyan jami’an ’yan sanda da ke kan aiki.

Sauran waɗanda suka halarci taron sun haɗa da wanda ya kafa ƙungiyar New Season Prophetic Prayers and Declarations, Fasto Jerry Eze; Shugaban Kamfanin Chrome Group, Cif Emeka Offor; da wasu mambobin Majalisar Dokoki.

Da yake bayanin shawarar komawa aikin lauya bayan shafe shekaru 34 yana aiki a rundunar ’yan sanda, Mba ya ce ƙwarewar da ya samu a fannonin jagoranci, ladabtarwa, sasanta rikice-rikice da gudanar da shari’a za ta taimaka masa matuƙa a sabon aikinsa. “Yin ritaya ba yana nufin ƙarshen hidima ba ne; dama ce ta ci gaba da hidima ta wata hanya daban. Shekarun da na yi a Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya sun ba ni ƙwarewa mai matuƙar amfani a fannonin jagoranci, ladabtarwa, sasanta rikice-rikice da gudanar da shari’a. Ina da niyyar amfani da waɗannan ƙwarewa tare da ilimin shari’a da na samu a wannan sabon babi na rayuwata,” inji shi.

Ya bayyana cewa shari’a ta wuce sana’a kawai, domin wata hanya ce ta kare haƙƙoƙin jama’a, sasanta saɓani, tabbatar da adalci da ƙarfafa amincewar al’umma ga hukumomi. A cewarsa, manufar kamfanin Frank Mba Legal ita ce gina kamfanin lauyoyi da kwastomomi za su iya amincewa da shi, wanda zai riƙa gudanar da ayyukansa bisa mafi girman ƙa’idojin ɗabi’a da ƙwarewa a aikin lauya.

Mba ya yi ritaya daga Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya a watan Maris na shekarar 2026, bayan shafe shekaru 34 yana hidima. A tsawon aikinsa, ya taɓa riƙe muƙamin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya har sau uku. Haka kuma, ya taɓa zama jami’in hulɗa da jama’a na rundunar a Jihar Legas, da kuma Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Ogun. Ya kuma jagoranci sashen horaswa da bunƙasa ƙwarewar jami’ai a matsayin mamba a tawagar gudanarwa ta rundunar, inda ya taka rawa wajen inganta ƙwarewar ma’aikatan ’yan sanda.

Komawarsa aikin lauya ya samo asali ne daga ilimin shari’a da ya samu a manyan makarantu. Ya yi digirin farko a fannin shari’a a Jami’ar Legas, sannan ya halarci Makarantar Koyon Aikin Lauya ta Nijeriya, inda ya samu lambar yabo. Daga bisani, ya yi digiri na biyu a fannin shari’a da ƙwararren sakamako a Jami’ar Dundee da ke ƙasar Scotland. An kuma karɓe shi cikin ƙungiyar lauyoyin Nijeriya a shekarar 2002, bayan kammala matakan da ake buƙata domin zama cikakken lauya.

Baya ga haka, Mba ya yi aiki a rundunar ’yan sandan Nijeriya da ta shiga aikin wanzar da zaman lafiya na Majalisar ɗinkin Duniya a Laberiya daga shekarar 2006 zuwa 2007, inda ya samu lambar yabo ta Majalisar ɗinkin Duniya bisa hidimar da ya yi.

By ukarofi

Leave a Reply