
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaban Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON), Ambasada Isma’il Abba Yusuf ya bayyana cewa, matakin amfani da dabarun fasahar zamani yana da matuƙar muhimmanci a harkokin aikin hajji musamman bisa la’akari da zamani da kuma ci-gaba.
Ambasada Isma’il Abba ya bayyana haka ne a taron Ƙungiyar Tallafa wa Aikin Hajji ta Ƙasa-da-ƙasa (IHFF) na 2026, wanda shi ne karo na takwas da aka gudanar, a birnin Jakarta da ke ƙasar Indonesiya. Hukumar kula da Kuɗaɗen Hajjin Ƙasar (Badan Pengelola Keuangan Haji – BPKH) ce ta jagoranci zaman a ɗakin taro na Jakarta International Convention Center.
A wannan shekarar, an yi wa taron take ne da “Sustainable Hajj Fund Management Through Strategic Synergy and Digital Transformatio,” wanda ya haɗa masu kafa tsare-tsare, ƙwararrun masu gudanar da kuɗaɗen shari’a da jagororin cibiyoyi.
A wata sanarwa da jami’in yaɗa labaran NAHCON, Shafi’i Sani Mohammed ya fitar a ranar Alhamis, 15 ga Oktoba, 2026, ya ce mahalarta taron sun tattauna akan hanyoyin da za a bi wajen warware matsalolin hauhawar farashin gudanar da harkokin aikin hajji da buƙatar samar da hanyoyin amfana da kuɗaɗen gudanarwa na tsawon lokaci.
Da yake jawabi a taron, Ambasada Yusuf ya yi tsokaci akan yadda za a shawo kan matsalolin yawan kashe kuɗaɗe a harkokin hajji musamman bisa abin da ya lura da shi a NAHCON, inda ya ce haɗin-gwiwa tsakanin hukumomi na taimakawa wajen rage matsalolin yawan kashe kuɗi a harkar.
Ya bayyana cewa, amfani da dabarun fasahar zamani za su taimaka wajen aiwatar da harkokin hajji bisa tsari kuma da taƙaice yawan kuɗaɗen gudanarwa, wanda hakan mataki ne na kare dukiya da tabbatar da ayyukan hajji na gaba sun amfana daga shirin bisa ci-gaba. Kazalika, ya ce amfani da dabarar faɗaɗa zuba jari a harkokin hajji musamman walwala da sauran lamuran da suka shafi jigilar alhazai, zuwa ƙaramin matakin kashe kuɗaɗe alama ce ta ci-gaba mai ɗorewa a fannin.



