ACF ga Ohanaeze da Afenifere: Ku bai wa ‘yan Arewa mazauna cikinku kariya

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar ‘Yan Arewa (ACF) ta yi kira ga takwarorinta na ƙabilar Ibo da Yarabawa, wato Ohanaeze Ndigbo da Afenifere, da su kauce wa abubuwan da ka iya cutar da rayuka da dukiyoyin ‘yan Arewa da sauran ‘yan ƙasa mazauna yankunansu, tare da cewa a nata ɓangaren za ta tabbatar da kariyar ‘yan ƙasa mazauna Arewa.

Cikin sanarwar bayan taron shugabannin ƙungiyar na ƙasa, shugaban ACF na ƙasa, Audu Ogbeh ya yaba wa ƙungiyar Ohanaeze dangane da nesata kanta da ta yi da harkokin IPOB da kuma shirin Eastern Security Network (ESN).

Ya ce nan ba da daɗewa ba ACF za ta kira taro da sauran ƙungiyoyin ƙabilu don tattauna matsalolin da ke fuskantar sassan ƙasa.

A cewar Ogbe said: “Ƙungiyar ta gamsu da matsayar da dattawan Kudu-maso-gabas da gwamnonin yankunan da ke neman kafa Biyafara
suka ɗauka. Ƙungiyar ta gamsu da yadda dattawan Ibo suka nesanta kansu tare da kira ga dattawan da su ɗauki ƙwararan matakai wajen kawo ƙarshen ƙudurin masu neman a raba ƙasa.

ACF ta ce tana bai wa ɗaukacin ‘yan ƙabilar Ibo mazauna Arewa tabbacin kare rayuwarsu.

Tana mai cewa, tana samun labari kullu yaumi game da yadda ake wahalar da ‘yan Arewa masu sana’a a Kudu, kamar masu yankan ƙumba, masu wanke takalma, ‘yan albasa, masu saida nama da sauransu, ana dukan na duka da kuma kashe na kashewa.

Ta ce tana fata waɗannan ‘yan Arewa da ke yankin su ma su samu kariya kwatankwacin yadda ‘yan Kudun ke samu a Arewa.

Ƙungiyar ta ce tana sa ran yin zama da shugabannin ƙungiyoyin Ohanaeze Ndi Igbo da Afenifere gami da shugabannin yankin Kudu-maso-kudu don tattauna matsalolin da ke haifar da rikicin ƙabilanci da na addini a faɗin ƙasa.

Daga nan, ACF ta yaba wa ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya da wasu gwamnoni irin su Atiku Bagudu na jihar Kebbi da takawaransa na jihar Barno, Babagana Umara Zulum, bisa ƙoƙarin da suke yi wajen yaƙi da ta’addanci a jihohinsu. Tare da yin kira ga sauran gwamnonin Arewa da su yi koyi da su.