Ba ni ke kashe kuɗaɗe kan matsalar tsaro a Zamfara ba, inji Kwamishinan tsaron jihar

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Kwamishinan ma’aikatar tsaro ta Jihar Zamfara, Amb. Bala Mairiga, ya musanta raɗeraɗin dake yawo a kafafen yaɗa labarai cewar gwamnatin jihar tana basu kuɗaɗe don magance matsalar rashin tsaro a fadin Jihar.

Kwamishinan yayi wannan tsokaci ne a wani faifan bidiyo a lokacin da yake ganawa da alummar garin sa na Talata Mafara.

Inason wannan faifan bidiyo a yaɗa shi kowa yasan halin da ake ciki, cewar ni babu hannun ma’aikata ta akan yadda ake kashe kuɗaɗe kan matsalar tsaro “. Inji shi.

Ya tabbatar da cewar gwamnatin jihar Zamfara tana iya ƙoƙarin ta wajen tabbatar da magance matsalar tsaro.

Yana mai nuni da cewar, ma’aikatar sa ƙarƙashin jagorancin sa sam ba ta da masaniya kan yadda ake kashe kuɗaɗe kan matsalar tsaro a jihar.

Kwamishinan ya zargi wasu makusantan gwamnatin Jihar da karɓe madafar ikon ma’aikatar tasa, yana mai jaddada cewar sune ke kula da yadda ake fitar da kuɗaɗe kan matsalar tsaro ba ma’aikatar tasa ba.

“Waɗannan mutanen ya kamata gwamnatin Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta Sani, ba masoyanta bane, maƙiyan ta ne Kuma suna yi mata zagon ƙasa ne”. Ya ƙara da cewa.

Yayi kira ga gwamnatin jihar da ta ɗauki matakin gaggawa don kawo sauyi mai inganci akan mutanen da yake zargin sune ke juya akalar gwamnatin jihar.

By ukarofi