Babu mai raba mana Nijeriya, cewar Ganduje

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya ce duk da irin matsalolin da Nijeriya ke fuskanta, za ta ci gaba da kasancewa ƙasa dunƙulalliya.

Ganduje ya bayyana haka ne a Kano a matsayin martani kan ce-ce-ku-cen da ake yi a ƙasa inda wasu ‘yan ƙasa ke rajin ɓallewa daga Nijeriya don kafa tasu ƙasar.

Gwamnan ya ce yana da yaƙinin Nijeriya ba za ta rabe ba komai ƙalubalen da take fuskanta.

Ya ci gaba da cewa ba ya son yin magana game da masu neman a raba ƙasa, saboda a cewarsa masu wannan buƙata matasa ne waɗanda ba su san mene ne yaƙin basasa ba.

Daga nan, Ganduje ya yaba wa ƙungiyar Ohanaeze Ndigbo saboda fitowa da ta yi ta nesanta kanta da harkokin masu rajin kafa ƙasar Biyafara.

Ta bakin Ganduje, “Ina da ƙwarin gwiwa saboda a makon da ya gabata, ƙungiyar Ohanaeze Ndigbo ta ce ba ta cikin masu neman kafa ƙasar Biyafara face tana daga cikin masu son dunƙulewar Nijeriya a matsayin ƙasa guda. Afenifere da Ƙungiyar Dattawan Arewa da kuma Ƙungiyar Arewa ta Tsayika, duk sun ce Nijeriya ɗaya ce.”

Da wannan ne Ganduje ya ce, “Ina kira ga dukkan ɓangarorin yankin da su haɗu su gano yadda za mu iya sauya bambancinmu zuwa ga tabbatar da haɗin kan ƙasar nan.”

Ya ce buƙatar da ke akwai shi ne girmama bambance-bambancen da ke tsakanin juna tare da sauya ƙalubalen da ake fuskanta zuwa haɗin kan al’ummomi da ma ƙasa baki ɗaya.