Babu ranar janyewa daga yajin aiki, cewar ASUU

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rahotanni sun ce an kasa cimma matsaya tsakanin ƙungiyar Malaman Jami’oi ASUU da Gwamnatin Tarayya, kan yajin aikin da ƙungiyar ta shafe matanni tana yi.

Tun watan Fabrairun 2022 ASUU ta shiga yajin aiki, haka ma ƙungiyar ma’aikatan jami’a sun shiga nasu yajin aikin daga baya kan wasu buƙatu da ƙungiyoyin suke son gwamnati ta cika masu.

Rahotanni sun ce ɓangarorin sun tattauna a ƙarshen mako, amma babu wata matsaya da aka cimma tsakanin shugabannin ƙungiyar malaman ASUU da ƙungiyar SSANU da NASU da kuma ɓangaren gwamnati, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Shugabannin ASUU sun ce gwamnati ta yi masu alƙawari tun watan Disamban 2020 amma har yanzu babu abinda aka yi, a cewarsu.

Kazalika Ƙungiyar Ɗalibai ta Nijeriya NANS sun yi barazanar yin zanga-zanga da rufe dukkanin hanyoyi da rumfunan zaɓen fidda gwani, matuƙar Gwamnatin Tarayya ba ta shawo kan lamarin yajin aikin da ya tilasta su zama gidajensu ba.

By Editor