Cigaba abu ne na zahiri a tarihin Sin

Daga CMG HAUSA

Shugaban Ƙasar Sin Xi Jinping, ya jagoranci taron tattauna ci gaban ƙasa da ƙasa jiya da yamma ta kafar bidiyo. Cikin jawabin buɗe taron, Xi Jinping ya bayar da labarinsa na kasancewa manomi a wani ƙaramin ƙauye dake yankin tsaunikan Loess na ƙasar Sin a ƙarshen shekarun 1960.

Wannan labari na shugaban ƙasar Sin ya bayyana cewa, ba tare da la’akari da inda suke ba, burin ɗaukacin mutane shi ne samun ingantacciyar rayuwa. Ga shugabanni kuwa, ci gaba da raya ƙasa ne kaɗai zai iya cimma burin jama’a na samun ingantacciyar rayuwa da zaman lafiyar al’umma.

Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa