Daga SANI AHMAD GIWA GIWA a Abuja
Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta dakatar da aiwatar da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke, wanda ya umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta soke rajistar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) da wasu jam’iyyun siyasa huɗu.
Jam’iyyun da hukuncin ya shafa sun haɗa da ADC, Action Peoples Party (APP), Action Alliance (AA), Accord Party (AP) da kuma Zenith Labour Party (ZLP).
A hukuncin da ta yanke, Kotun Daukaka Kara ta amince da buƙatar dakatar da aiwatar da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta bayar, tare da hana duk wani yunƙuri na aiwatar da umarnin soke rajistar jam’iyyun har sai an kammala shari’ar da ke gabanta.
Kotun ta kuma yi kakkausar suka ga yadda alƙalin Babbar Kotun Tarayya, Mai Shari’a Peter Lifu, ya gudanar da shari’ar, tana mai cewa ya yi hakan ne duk da cewa akwai umarnin Kotun ɗaukaka ƙara da ke hana ci gaba da sauraron ƙarar.
Alƙalan kotun sun bayyana cewa alƙalin ya ci gaba da sauraron shari’ar tare da yanke hukunci alhali har yanzu ƙarar na gaban kotun da ta fi ta ƙarfi, lamarin da suka ce ya saɓa wa tsarin matakan shari’a da kundin tsarin mulkin ƙasa.
A cewar kotun, matakin da alƙalin ya ɗauka ya nuna rashin mutunta tsarin shari’a da matsayi na manyan kotuna.
“Kotuna na da alhakin kare mutuncinsu. Wannan kotu tana da ikon sa ido kan ayyukan kotun da ke ƙarƙashinta. Ci gaba da yanke hukunci duk da umarnin da wannan kotu ta bayar babban saba wa tsarin kotuna ne da kuma kundin tsarin mulkin shekarar 1999,” inji kotun.
Kotun ta ƙara da cewa tana da ikon tabbatar da cewa ana biyayya ga umarninta, saboda haka ta amince da buƙatar dakatar da aiwatar da hukuncin.
“An amince da buƙatar dakatar da aiwatar da hukuncin. Saboda haka, an dakatar da aiwatar da hukuncin da aka yanke,” inji alƙalan.
Tun farko dai Babbar Kotun Tarayya ta yanke hukuncin cewa jam’iyyun ADC, APP, AA, AP da ZLP ba su cika sharuddan da kundin tsarin mulki ya gindaya ba domin ci gaba da kasancewa a matsayin jam’iyyun siyasa masu rajista.
Kotun ta ce jam’iyyun sun kasa cimma matakan da doka ta tanada dangane da sakamakon zaɓuka da kuma wakilci a muƙaman siyasa.
Sai dai da wannan sabon hukunci na Kotun ɗaukaka ƙara, an dakatar da aiwatar da umarnin soke rajistar jam’iyyun, yayin da ake jiran hukunci na karshe kan rikicin shari’ar.
Wannan mataki na nufin cewa jam’iyyun da abin ya shafa, ciki har da ADC, za su ci gaba da kasancewa a matsayin jam’iyyun siyasa masu rajista har sai an kammala dukkan matakan shari’ar.
