Ma’auratan Kaduna da jaririyarsu ‘yar wata shida sun shaƙi iskar ‘yanci

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Malam Ahmed Abubakar Zakka da matarsa da ‘yarsu mai wata shida, Fatima, sun shaƙi iskar ‘yanci bayan shafe kwanaki a hannun ‘yan bindiga. A cewar majiyoyi, an sako mutanen ne a ranar Alhamis kuma suna kan hanyar komawa cikin garin Kaduna a lokacin da ake haɗa wannan rahoto.

Saidai ba a samu cikakken bayanin yadda al’amarin kuɓutarsu daga hannun ‘yan bindigar ta kasance ba, amma wani jami’in tsaro mai ritaya da ke aiki da tawagarsa domin ceto ma’auratan ya tabbatar da wannan ci-gaba ga wakilinmu. Jami’in, wanda ya nemi a sakaye sunansa, ya ce mutanen suna kan hanyar koma wa gida tare da direbansa a wata mota.

An yi awon-gaba da mutane ukun ne a gidansu da ke yankin unguwar Millennium City a Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna a ranar 6 ga Oktoba, 2026.

Wani faifan bidiyo ya nuna yadda Ahmed Zakka da ‘yar da matar tasa suke hannun masu garkuwar, wanda ya karaɗe shafukan sada zumunta kwanaki kaɗan da yin garkuwa da su, lamarin da ya haddasa cece-kuce a sassan Nijeriya.

By Babaji

Leave a Reply