Masanan ƙasar Sin na cigaba da gabatar da abubuwa na ban mamaki ga duniya

Spread the love

Daga FAEZA MUSTAPHA

A karon farko, ƙasar Sin ta ƙaddamar da wata sabuwar tashar samar da lantarki daga hasken rana da ƙarfin igiyar ruwa, wadda ke da ƙarfin samar da lantarkin da ya zarce kilowatt miliyan 100 cikin shekara guda.

Haƙiƙa wannan wani ƙarin nasara ce ga ƙasar Sin a ƙoƙarin da take ci gaba da yi na rage fitar da hayaƙi mai gurɓata muhalli. Haka kuma nasara ce ga duniya domin ta gabatar musu wani abun misali da koyi a ɓangaren amfani da makamashi mai tsafta domin raya muhalli da biyan buƙatun al’umma.

Abun da ya burge ni cikin wannan sabuwar fasaha shi ne, yadda aka haɗa hasken rana da ƙarfin igiyar ruwa. Wato za a samu makamashi a lokacin da rana ta kwalle daga haskenta, yayin da idan dare ya yi, za a samu makamashi daga ƙarfin igiyar ruwa, ta yadda a ko da yaushe, ba za a raba rasa makamashi ba. Ba shakka, masanan ƙasar Sin na ci gaba da gabatar da sabbin abubuwa na ban mamaki masu ma’ana da aminci ga al’ummar duniya.

Duk da irin ci gaban da Sin ta samu, har yanzu ba ta gajiya ba, tana ƙara ƙoƙarin kirkiro sabbin fasahohi da nufin biyan buƙatun al’ummarta, lamarin dake ci gaba da nuna yadda walwalar al’ummarta ke kasancewa kan gaba a cikin manufofinta. Misali, wannan tasha za ta biya buƙatar lantarki na gidaje kimanin 30,000 na birnin Wenling dake lardin Zhejiang.

Hasken rana da igiyar ruwa, albarkatu ne da kowacce ƙasa ba za ta rasa ba, musamman ma ƙasashenmu na Afrika. La’akari da yadda ake fama da rashin lantarki a ƙasashen, kamata ya yi su ƙara kyautata hulɗarsu da ƙasar Sin domin koyon dabarunta. Ƙasar Sin ita ce mafi yawan al’umma a duniya, amma duk da haka, al’ummarta na cikin walwala saboda jajircewarta.

A ganina, sauran ƙasashe masu tasowa ba su da wani dalili na rashin kyautata walwalar al’ummarsu. Ya kamata ci gaban ƙasar Sin ya zama mai ba su ƙwarin gwiwa.

By Editor