Wanda ya tsara tutar Nijeriya ya cika shekara 85 da haihuwa

A bana Chief Michael Taiwo Akinkunmi, OFR, ya cika shekara 85 da haihuwa.

Akinkunmi shi ne talikin da ya tsara tutar Nijeriya kamar yadda ake ganin ta a yau.

Tuni ‘yan ƙasa suka shiga yi masa fatan alheri bisa zagayowar ranar haihuwarsa tare da yaba wa fasaharsa wajen samar wa Nijeriya tuta mai tsari wadda ta samu karɓuwa da tagomashi a faɗin duniya.