Mayaƙan Boko Haram-ISWAP 45 sun miƙa wuya a Konduga

Mayaƙan Boko Haram da ISWAP a ƙalla su 45, ciki har da ƙananan yara da matasa, suka tuba suka miƙa wuya ga sojoji a yankin Arewa-maso-gabas.

Mayaƙan sun miƙa wuya ne a Litinin da ta gabata a yankin Ƙaramar Hukumar Konduga a jihar Borno.

Sai dai, wata majiya ta kusa sa sojojin ta ce mayaƙan sun miƙa wuya ne ba tare da miƙa makamansu ba.

A cewar majiyar, waɗanda lamarin ya shafa 21 daga cikinsu daga Garin Dinya suke, sannan 24 daga ƙauyen Jaja Kalwa.

Wasu mutum biyar daga cikin mayaƙan sun shaida wa jaridar PRNigeria cewa, an tilasta su ne suka shiga ƙungiyar ‘yan ta”addar.

Wani mai suna Modu Malaram daga Jaja Kalwa ya ce, “Wallahi, galibinmu mun yi ƙanana, ko kuma ba mu da ƙarfin da za mu yaƙi kwamandojin Boko Haram da suka kwashe mu daga ƙauyukanmu.

“Tun farko muna sane da ƙungiyoyin miyagu ne amma ba mu iya faɗa da su ba saboda yin hakan ka iya sa mu rasa ranmu. Wasu da suka yi yinƙurin tserewa daga cikinmu an halaka su.”

Malaram ya ci gaba da cewa, “Duk cewa ni da matata da ɗana mun tuba, ba na ganin mutanen ƙauyenmu za su aminta da mu kuma.”

Game da ko me ya sa suka fito suka bayyana tubansu, Malaram ya ce hakan ya faru ne sakamakon rarrabuwar kai a tsakanin jagororin ɓangarorin biyu tun bayan mutuwar Shekau wanda hakan ya sa shi da ire-irensa suka zaɓi bayyana tubansu.

Jaridar PRNigeria ta gano cewa akwai yiwuwar a samu ƙarin mayaƙan da dama da suka za su miƙa wuya ga sojoji a ‘yan kwanaki masu zuwa.