Daga CMG HAUSA
Mamban majalisar gudanarwar ƙasar Sin kana ministan harkokin wajen ƙasar Wang Yi ya bayyana a jiya Lahadi cewa, ƙasar Sin za ta ƙara faɗaɗa da zurfafa bude kofa ga ƙasashen waje, kuma tana son raba sakamakon ci gaban da ta samu da ƙasashen tsibirin Pacific.
Wang ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da Henry Puna, babban sakataren dandalin tattaunawar tsibiran Pacific, a Suva, babban birnin ƙasar Fiji.
Fiji ne zango na huɗu, a rangadin aiki na kwanaki 10 da Wang Yi ke yi, bayan ziyarar da ya kai tsibirin Solomon, da Kiribati da Samoa. Jami’in diflomasiyyar na ziyarar aiki a ƙasar Fiji, inda kuma zai jagoranci taron ministocin harkokin wajen ƙasashen Sin da na tsibirin Pasifik karo na biyu.
Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa
