Sojoji sun kama wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne a wani masallacin Kano

Daga UMAR M. GOMBE

Sojojin Nijeriya sun kai samame a wani masallaci da ake zargin na ‘yan Boko Haram ne da ke Hotoro a Kano, inda suka cafke wasu mutum 10.

Bayanan da Manhaja ta kalato sun nuna an yi kamen ne da yammacin Asabar da ta gabata.

Haka nan cewa sojojin sun aiwatar da aikinsu ne cikin ƙwarewa ba tare da ɗaga hankali kowa ba da ke yankin.

Rahotanni sun suna wasu da suka yiwo gudun hijira daga Barno zuwa Kano a dalilin rikicin Boko Haram ne suka kafa masallacin.

Ya zuwa haɗa wannan labari, da aka nemi jin ta bakinsa game da lamarin, Mai Magana da Yawun Sojoji a Kano, Captain Uba, ya ce batun bai iso gabansa ba tukuna, amma cewa duk halin da ake ciki zai yi magana a gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *