Sojoji sun yi artabu da tserarrun ‘yan bindigar Zamfara a Neja

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Jami’an tsaron haɗin gwiwa na Nijeriya sun kasha aƙalla ‘yan bindiga 32 da suka tsere daga Zamfara a jihar Neja.

Hakan ya faru ne bayan da ‘yan bindigar suka kai hari kan ofishin tsaro, suka harbe ‘yan sanda biyar da suka yi ƙoƙarin fuskantar su.

Lamarin ya faru ne a Bangu Gari da ke ƙaramar hukumar Rafi ta jihar.

Wata majiyar tsaro ta shaida wa manema labarai cewa, ‘yan bindigar da suka tsere daga jihar Zamfara saboda ayyukan da sojoji ke yi, da farko sun yi ɓarna a cikin al’umma.

Majiyar ta ƙara da cewa, “’yan bindigar sun zo da yawa tare da manyan makamai ciki har da masu harba roka bayan sun tsere daga sansaninsu a Danjibga da Munhaye a qaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

Sun kai hari ofishin ‘yan sanda da ke Bangu Gari a ƙaramar hukumar Rafi kuma sun kashe ‘yan sanda biyar yayin musayar wuta. Nan da nan aka karɓi sigina kuma aka aika da rundunar tsaro ta haɗin gwiwar Sojojin da aka ƙara musu ƙarfin gwiwa inda suka yi nasarar fatattakar ‘yan ta’addan yayin da suke ƙoƙarin tserewa ta hanyar Tegina,” inji magiyar.”

“Aƙalla 32 daga cikin ‘yan bindigar sun mutu ciki har da shugabanninsu, Karki Buzu da Yalo Nagoshi yayin da wani sarkin, Ali Kawaji ya samu munanan raunuka na bindiga,” inji majiyar.