Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kakakin Majalisar Wakila ta Nijeriya, Tajudeen Abbas, ya bayyana cewa yanzu ya zama wajibi ’yan Nijeriya su fara cin moriyar gyare-gyaren tattalin arzikin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar, ta hanyar inganta ayyukan gwamnati, samar da ayyukan yi da kuma kyautata rayuwar al’umma.
Abbas ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban ƙasa a 2027 a Abuja, inda ya ce dakatar da gyare-gyaren kafin a cimma nasarar da ake fata na iya kawo cikas ga ci gaban da aka samu.
Ya amince cewa matakan sauye-sauyen tattalin arzikin sun jefa gidaje da ’yan kasuwa cikin matsin lamba, amma ya jaddada cewa lokaci ya yi da gwamnati za ta mayar da ƙarin kuɗaɗen shigar da take samu zuwa ayyukan raya ƙasa da jama’a za su gani kuma su amfana da su.
A cewarsa, “Wa’adin farko ya fuskanci matsalolin rashin daidaito, tare da faɗaɗa kuɗaɗen shigar gwamnati. Wa’adi na biyu kuwa dole ne ya mayar da waɗannan kuɗaɗen zuwa amfanin jama’a. Nijeriya ta biya kuɗin gyare-gyaren tattalin arziki, don haka yanzu dole ne ta fara cin moriyar sakamakonsu.”
Kakakin Majalisar ya ce ci gaba da manufofin gwamnatin na buƙatar mayar da hankali sosai kan rage wa jama’a raɗaɗi, faɗaɗa damar samun ayyukan yi da kuma inganta muhimman ayyukan more rayuwa.
Abbas ya ambaci wasu alƙaluma da ya danganta da rahotannin baya-bayan nan na Bankin Duniya, ciki har da bunƙasar tattalin arzikin Nijeriya da kashi 4.2 cikin 100 a farkon rabin shekarar 2026, da kuma ƙaruwar ajiyar kuɗaɗen ƙasar waje zuwa sama da dala biliyan 54 a watan Satumbar 2026.
Haka kuma, ya ce Nijeriya ta samu rarar ma’amalolin asusun ƙasa da ƙasashen waje ta yanzu (current account surplus) ta dala biliyan 12, yayin da hajojin da ba na man fetur ba da ƙasar ta fitar zuwa ƙasashen waje suka haura dala biliyan shida a shekarar 2025.
Ya ƙara da cewa kuɗaɗen shigar gwamnatin tarayya sun ƙaru da kashi 69 cikin 100 a zahiri tsakanin shekarar 2023 zuwa 2025, yayin da kuɗaɗen shigar gwamnatocin jihohi suka ƙaru da kashi 93 cikin 100.
A cewarsa, duk da waɗannan nasarori, abin da zai fi muhimmanci shi ne yadda sauye-sauyen za su inganta rayuwar ’yan Nijeriya kai tsaye.
Ya buƙaci a riƙa kare gwamnati da sahihan bayanai
Abbas ya ƙalubalanci jam’iyyun adawa da su gabatar da manufofi da za su zama ingantattun madadin na gwamnati, sannan ya buƙaci masu goyon bayan gwamnatin Tinubu su riƙa kare ta ta hanyar amfani da sahihan bayanai.
Ya ce masu kare gwamnati ba sa buƙatar ƙirƙirar hujjoji, sai dai su gabatar da ingantattun bayanai domin amsa suka daga abokan hamayya.
“Jakada ba ya ƙirƙirar hujjoji. Idan abokan hamayya suka ɗaga muryoyinsu, mu kuma ya kamata mu ƙara ingancin hujjojinmu,” inji shi.
Da yake magana kan ayyukan Majalisar Wakilai ta 10, Abbas ya ambaci dokokin da suka shafi lamunin karatu ga ɗalibai, mafi ƙarancin albashi na ƙasa, gyaran tsarin haraji da kuma abin da ya bayyana a matsayin Dokar Zaɓe ta 2026.
Ya ce Majalisar Wakilai ta karɓi ƙudurin dokoki 2,747, inda ta amince da 363, daga cikinsu fiye da 70 sun samu amincewar shugaban ƙasa.
Ya kuma bayyana ƙoƙarin da majalisar ke yi wajen samar da tubalin doka domin kafa rundunar ’yan sandan jihohi.
A cewarsa, wajibi ne ’yan majalisa su samar da dokokin da za su bai wa gyare-gyaren gwamnati damar yin nasara, tare da tabbatar da cewa ana riƙe gwamnati da alhakin sakamakon manufofinta.
Ya ƙara da cewa zaɓen shekarar 2027 zai bai wa ’yan Nijeriya damar tantance ayyukan gwamnatin Tinubu da kuma yanke shawarar ko manufofinta sun cancanci sake ba ta wani wa’adi.
A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya shawarci Shugaba Tinubu da ya ci gaba da kyautata alaƙarsa da abokan tafiyarsa na siyasa yayin da shirye-shiryen zaɓen 2027 ke ƙara nisa.
Akpabio ya ce haɗin kai tsakanin shugabannin siyasa da ’yan Majalisar Tarayya yana da muhimmanci wajen isar da saƙon shugaban ƙasa na haɗin kai da sauya Nijeriya zuwa ga ’yan ƙasa.
Ya kuma ba da shawarar cewa a yi la’akari da shigar da ’yan jam’iyyun adawa da ke cikin ɓangaren marasa rinjaye a majalisa cikin wannan shiri, domin faɗaɗa haɗin gwiwar siyasa.
